Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 162 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Asabar.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Asabar sun nuna cewa jihar Legas ta samu karin mutum –26,Gombe-54, FCT-35, Ogun-12, Filato-10, Rivers-10, Kaduna-4, Ekiti-3, Edo-2, Osun-2, Bayelsa-1, Imo-1, Ondo-1 da Oyo-1
Yanzu mutum 62,853 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 58,675 sun warke, 1,144 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 3,034 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 21,238, FCT –6,088, Oyo – 3,448, Edo –2,666, Delta –1,814, Rivers 2,820, Kano –1,747, Ogun –2,043, Kaduna –2,652, Katsina -952, Ondo –1,667, Borno –745, Gombe – 883, Bauchi – 713, Ebonyi –1,049, Filato -3,640, Enugu – 1,314, Abia – 898, Imo –616, Jigawa – 325, Kwara – 1,069, Bayelsa – 413, Nasarawa – 482, Osun –928, Sokoto – 165, Niger – 274, Akwa Ibom – 295, Benue – 493, Adamawa – 252, Anambra – 277, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 79, Ekiti – 335.
Taraba- 146, Kogi – 5, da Cross Rivers – 87.
Yaran Makaranta 181 da malamansu sun kamu da Korona a wani makaranta a Legas
Akalla dalibai da malaman su 181 ne aka tabbatr sun kamu da Korona da wani makaranta mai zaman kansa a Legas.
Ma’aikatar kiwon Lafiya ta jihar Legas ta sanar cewa yaran makaranta 181 da wasu malaman su sun kamu da Korona a wani makarantar Kwana dake Lekki, Jihar Legas.
Kwamishinan Lafiya na jihar Akin Abayomi, ya shaida cewa bincike da aka gudanar ne ya sa aka gano wadanda suka kamu da cutar.
” Wata daliba ‘yar ajin SSII ce ta fara rashin Lafiya, da aka kaita asibitin makarantar, a nan ne aka gano ta Kamu da Korona. Da aka yi wa daliban makarantar gwaji sai aka gano yara 181 duk sun kamu da wasu daga cikin malaman su.
” Sai dai cutar bata kwantar da su ba dukkan su. Mun shawar ce su da su cigaba da zama a makarantar kada kuma su koma gida su yada cutar, sannan kuma mun tura malaman lafiya su ci gaba da samar da kula a wurin da kewaye.”