Sojojin kundumbalar Amurka da aka fi sani da SEAL, sun kwato Ba’Amurken da aka yi garkuwa da shi a Arewacin Najeriya.
An yi garkuwa da Walton a Nijar, amma aka ceto shi a wani gari cikin Areacin Najeriya.
Phillip Walton dan kasar Amurka ne da aka tsare a Arewacin Najeriya, aka nemi mahaifin sa ya biya diyya, tun a ranar 26 Ga Oktoba ake tsare tsare da shi.
Kwamandojin Zaratan Sojojin Kundumbala na SEAL ne su ka ceto dan shekara 27 din da jijijifin safiyar Asabar, 31 Ga Oktoba.
Jami’an yaki da ta’addancin Amurka ne su ka tabbatar wa gidan talbijin na ABC da ke Amurka wannan labari.
Sannan ita ma jaridar Sun ta London ta buga rahoton cewa wadanda su kayi garkuwa da Walton, sun kira mahaifin sa wanda ba shi da nisa da inda su ka kama dan na sa a wata gona a Nijar, su ka bukaci ya biya makudan kudade domin a sako dan na sa.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ceto Walton dan kasar daga ‘yan bindiga a Najeriya da kwamandojin SEAL su ka yi, wata babbar nasara ce ga jami’an SEAL da Amurka baki daya.
Kakakin Cibiyar Tsaron Amurka Pentagon, Jonathan Hoffman, ya shaida karin hasken cewa da jijifin asubahin ranar 31 Ga Oktoba sojojin su su ka dirar wa mahara su ka ceto dan kasar na su.
“Babu wabi sojan Amurka ko daya da ji rauni. Mu na godiya hadin kan da takwarorin mu na wasu kasashe su ka bayar har mu ka kai farmakin ceto dan kasar ta mu.” Inji Hoffman cikin sanarwar da ya fitar wa manema labarai.
Shi ma Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo, ya jinjina wa zaratan sojojin da su ka ceto Walton.
“Ina godiya ga jami’an sojojin da su ka yi wannan gagarimin aikin ceto. Kuma mu na godiya ga sauran kwararru da jami’an diflomassiyya. Wanda aka yi garkuwa da shi din zai sahu da iyalin sa ba da dadewa ba. Ba za mu taba yin watsi mu kyale wani Ba’Amurke a hannun masu garkuwa ba.”
Sai dai kuma sanarwar ba ta bayyana ko masu garkuwa nawa sojojin Amurka su ka kashe a Arewacin Najeriya, kafin su ceto dan kasar su din ba.