Bashin da ke kan Najeriya zai kai naira tiriliyan 38.68 nan da Disamba 2021 – Ministar Kudi

0

Ministar Harkokin Kudade Zainab Ahmed, ta tabbatar da cewa tulin bashin da ke kan Najeriya zai kai naira tiriliyan 38.68 nan da watan Disamba, 2021.

Zainab ta yi wannan kintacen ne ranar Talata a gaban Kwamitin Bin Biddigin Basussukan Cikin Gida da Waje da ake bin Najeriya, a zauren Majalisar Dattawa.

An gayyaci Zainab ne domin yi wa kwamiti karin haske dangane da tulin bashin da ake bin Gwamnatin Tarayya da Jihohi 36 har da FCT Abuja.

Hakan kuwa ya biyo bayan yawan damuwar da ake nunawa dangane da yawan wadannan tulin basussukan.

Gwamnatin Buhari dai ta shirya ciwo bashin naira tiriliyan 4.28, domin cike gibin kasafin 2021, wanda Najeriya ba ta da isassun kudaden gudanar da ayyukan kasafin.

Kenan kashi 1/3 na kasafin 2021, duk sai an ciwo bashi sannan za a iya yin ayyukan.

Cikin watan Oktoba ne Buhari ya gabatar da kasafin 2021, na naira tiriliyan 13.08.

To sai dai kuma kintacen kudaden shigar da gwamnatin ta ce za iya tarawa, bai wuce naira tiriliyan 7.886 ba. Saboda haka tilas sai an yi buga-bugar nemo bashin naira tiriliyan 4.28 kenan.

Halin Da Ake Ciki A Yanzu:

Ministar Harkokin Kudade, Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arzikin Kasa, Zainab Ahmed ta ce a yanzu dai bashin da ake bin Gwamnatin Tarayya, Jihohi 36 da kuma Gundumar FCT Abuja, a jimlace ya kai naira tiriliyan 31.01, daidai da dala biliyan 85 kenan.

Ta ce wannan kididdiga ce fa tun ta ranar 30 Ga Yuni, wadda daga lokacin ba a sake bin diddigi ba.

Dalili kenan ta ce idan aka kai karshen 2021, aka hada da basussukan da Najeriya za ta kara ciwowa, adadin zai kai naira tiriliyan 38.68.

Ayyukan Manyan Titina Za Su Shiga Garari:

Minista Zainab ta shaida wa Kwamitin Kula Da Basussuka cewa akwai matsalar kudi sosai da ta daskare ayyukan manyan titina, kuma a wannan kasafin kudi na 2021 ma a haka abin zai kasance, matukar Najeriya ba ta canja taku ba.

Shawarar da ta bayar ita ce, a daina kwasar ayyukan titina da yawa ana bayarwa kwangila.

Ta ce kamata ya yi a samu shiyya daya a dauki titi daya a bayar da kwangilar sa. Kada a bayar da kwangilar gina wani titin har sai an kammala wancan tukunna.

Ta buga misalin yadda ayyukan titina ke tafiyar hawainiya da cewa, “za a bada aikin naira bilyan 10. Sai an fara ka ga dan kwangila ya zo ya na keman karin kudi. Daga nan idan aka yi buga-buga aka ba shi naira milyan 100, to idan ya je ta kare kuma sai aikin ya tsaya, har sai an sake lalubo wasu kudin an ba shi.”Bashin da ke kan Najeriya zai kai naira tiriliyan 38.68 nan da Disamba 2021 -Zainab, Ministar Kudi.

Share.

game da Author