An kori malaman firamare da na sakandare 71 a makarantar Hukumar SSS

0

Akalla malaman firamare da na sakandare 71 ne aka yi wa korar-bazata a sakandaren Community Staff School, mallakar Jami’an SSS a Abuja.

Sallamar ta su ta biyo bayan kukan da su ka yi na neman inganta kula da su, wanda a lokacin da su ka fito nuna damuwar ta su, har tarwatsa su aka yi, ta hanyar dankara harbi a sama domin a razana su.

Takardar sallamar da aka raba wa kowane malamin mai dauke da ranar 2 Ga Nuwamba, ta fado kan teburin PREMIUM TIMES.

Da farko kafin a sallame su, an umarci iyayen dalibai cewa kowane yaro ya zauna a gida tsawon makonni biyu, domin a samu damar yi wa makarantar gyare-gyare.

Sai dai kuma abin da ya biyo bayan wannan, shi ne sanarwar sallamar dukkan malaman makarantar, na firamare daga hedimasta zuwa kowa da kowa.

An kuma koma bangaren sakandare aka sallami run aga firincifal har zuwa mai aiki dakin gwaji.

“Shugaban Hukumar SSS ya ba ni umarnin sanar da sallamar su daga aiki. Wannan ya faru ne saboda matsalar kuncin tattalin arziki da ya faru saboda korona.”

Sanarwar ta umarci duk mai wani abu mallakin makarantar, ya gaggauta damkawa ga hukumar makarantar.

Malaman sun dade su na kokawa kan rashin kula. Sannan su kuma iyayen yara sun koka saboda duk da halin da ake ciki, an yi karin kudin makaranta daga naira 70,000 zuwa naira 90,000.

Su kuma malamai sun ce an zaftare masu albashi da wasu hakkokin da su ka nema aka yi masu.

Share.

game da Author