Za a cigaba da jarabawar NECO daga ranar 9 ga Nuwamba

0

Hukumar Shirya Jarabawar Kammala karatun Sakandare (NECO), ta bayyana cewa za a cigaba da rubuta jarabawar a jihohi 36 da Abuja daga ranar 9 ga Nuwambar 2020.

Hukumar ta Kuma fidda sabuwar jadawalin jarabawar wanda dalibai za su yi amfani da shi.

Kakakin hukumar Azeez Sani ya Sanar da haka a wani takarda da aka raba wa manema labarai ranar Litini.

Sani ya ce za a iya samun wannan sabuwar jadawalin jarabawar a shafin hukumar na yanar gizon a ‘www.neco.gov.ng’ ko kuma a ofishin su daga ranar 4 ga Nuwanba.

A ranar 19 ga Oktoba ne PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa hukumar NECO ta dage ranar fara Jarabawar da za a fara ranar 19 ga Oktoba zuwa 16 ga Nuwamba.

A wannan ranar ne hukumar ta tsaida don fara jarabawar amma ta maida shi zuwa ranar 17 Ga Nuwamba.

Azeez Sani, ya ce an matsa da jarabawar zuwa gaba ne saboda zanga-zangar #EndSARS da ya rusa tsarin da aka yi da farko.

Ya ce zanga-zangar wanda ta takaita zirga-zirgar motoci ta kawo tsaiko da cikas wajen raba kayan jarabawa a fadin kasar nan.

Share.

game da Author