Dan takarar zaben gwamnan jihar Ondo a karkashin jam’iyyar PDP, Eyitayo Jegede, ya ce kalubalen da ya fi damun sa kadai a zaben da ake kan gudanarwa, shi ne yadda ake ta samun yawan kakarewar da na’urorin tantance katin rajista, wato ‘card readers’ ke yi.
Haka ya bayyana wa manema labarai bayan ya kammala jefa kuri’a a Mazabar da ke cikin makarantar Sacred Health Primary School da ke Akure ta Kudu.
Ya ce kakarewar da na’urorin ke yawan yi ya kawo tsaiko da bata lokaci sosai wajen jefa kuri’a.
Sai dai kuma ya yaba da dimbin masu jefa kuri’a da su ka fito domin su jefa kuri’a ga wanda hankalin su ya kwanta su zaba.
“Na dade tsaye a kan layi. Kuma tabbas na nuna wa jami’an zabe rashin jin dadin abin.
“An ce min na’ura ta kakare, amma na ce ba zan yi zaben ‘yar-tinki ba, sai da ‘card reader.’ Na yi tsaye kikam sama da minti goma sannan na’urar ta fara aiki.” Inji Jegede, wanda ya ce a iyar abin da ya gani dai ana zabe lami lafiya.
Sai dai kuma ya ce ya samu labarin tashe-tashen hankula a Ijomu, cikin Karamar Hukumar Akure ta Kudu, wato karamar hukumar sa.
“Mun ji wannan labarin kuma mun ga inda wasu mutane da ake ganin masu mutunci ne su na halayyar ‘yan jagaliya.” Inji Jegede.
Kakakin Yada Labarai na ‘Yan Sandan Ondo, Tee Leo-Ikoro ya ce wa PREMIUM TIMES ba a yi wani tashin hankali a inda Jegede ya yi ikirari ba.
Wannan ne karo na biyu da Jegede ke tsayawa takarar gwamnan Ondo. A zaben 2016 ya tsaya, amma Rotimi Akeredolu ya kayar da shi.