Rundunar ‘Yan Sandan Ondo ta bada sanarwar cewa ta damke jami’in ta daya, bayan ya karya dokar zaben da ta haramta wa dogaran manyan masu mulki su janye daga raka su zuwa wurin dangwala kuri’a.
An kama dan sandan bayan ya raka Alaba Lad-Ojomo zuwa dangwala kuri’a a Mazabar Owo, cikin Karamar Hukumar Owo.
Alaba ya taba yin Dan Majalisar Tarayya har sau biyu. Kuma har yanzu ba a bayyana suna da mukamin dan sandan ba.
A lokacin da wakilin mu isa wurin, ya iske ana ta markabu, shi kuma Lad-Ojomo na ta rokon wani babban jami’in dan sanda cewa ya saki dogarin na sa.
Sai dai a gaban wakilin mu babban dan sandan ya ce, “ba zan sake shi ba. Saboda ya yi rashin da’a.”
Daga nan Lad-Ojomo ya fusata, ya rika zazzafar cacar-baki da babban dan sandan. A karshe ya bar wurin cikin fushi, ganin cewa an ki sakar masa dogari.
Lad-Ojomo ya yi majalisar tarayya a zaben 2003 da 2011. Daga nan kuma ya yi ta kokarin zama shugaban jam’iyyar PDP a jihar Ondo a 2020.
Wani da aka yi abin a gaban sa, amma ba ya so a ambaci sunan sa, ya ce, “dan sandan da aka damke din ya cika girman kai da fankama da tinkaho.”