Shugaban Amurka Trump da matar sa sun kamu da cutar Korona

0

Shugaban Amurka Donald Trump da matar sa Melania sun kamu da cutar Coronavirus a daren Juma’a.

Sanarwar da Trump ya yi da jijjifin asubahin nan, ya tabbatar da cewa shi da matar sa sun kamu da cutar.

A shafin sa Twitter ya yi sanarwar, ya na mai cewa, za su killace kan su har zuwa lokacin da likitoci su ka tabbatar da cewa sun warke garas.

“Mata ta da ni mun kamu da cutar Coronavirus, don haka za mu killace kan mu har zuwa lokacin da mu ka wartsake…..” Haka ya bayyana a shafin sa na Twitter.

Trump ya kamu da cutar daidai lokacin da ake wutar kamfen din yakin neman zaben shugaban kasa da za a gudanar cikin watan Nuwamba.

Kafin nan sai da aka bayyana cewa Hadimin Trump Hope Hicks ya kamu da cutar. Hicks da shi aka raka Trump wurin gwabza muhawara da dan takarar jam’iyyar Democrat, Joe Biden a ranar Talata.

Coronavirus ta kashe sama da mutum 200,000 a Amurka.

Trump ya kamu da cutar bayan ya dade ya na kalamai na sosa ran jama’a dangne da cutar. Kuma ya rika maida batun ta kamar abin zolaya.

A ranar da ya yi muhawara da Biden, Trump ya rika gwasale shi saboda ya na daura takunkumi a baki. Trump ya rika bugun kirjin cewa shi babu ruwan sa da daura takunkumi.

Watannin baya Trump ya samu takun-saka da Shugaban Hukumar Kula da Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, har ya yi barazanar janye tallafin da Amurka ke bai wa WHO din.

Yayin da Coronavirus ta kama Amurka bagatatan, Trump ya rika yi wa likitoci katsalandan, har ya na cewa a yi wa mutane allurar ruwan sabulun wanke hannu kawai, za a ga magani gangariya a wannan dabarar.

Kamuwar da Trump ya yi da cutar Coronavirus ta tsayar da kamfen din sa cak, kuma ta dakatar da sauran muhawara biyu da zai yi tare da Biden.

Share.

game da Author