Ministan Ilmi Adamu Adamu ya bayyana cewa gwamnati ta amince makarantun kasar nan kaf su koma karatu bayan watanni 7 da suka yi a kulle saboda annobar Korona.
Ya ce kwalejojin dake karkashin gwamnatin tarayya wato ‘Unity Colleges’ za su koma makaranta ranar 11 ga Oktoba.
Yace makarantu masu zaman kansu da na gwamnati a jihohi kuma, jihohin za su sanar musu da ranakun komawa.
Sai dai kuma minista Adamu ya ce dole sai an ci gaba da kiyaye dokokin Korona domin kare ɗalibai daga kamuwa da cutar.
Jihar Kano
Kwamishinan ilimin jihar Kano Muhammad Kiro ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta amince ɗalibai su koma makarantu domin ci gaba da karatu daga ranar 11 ga Oktoba.
Kwamishinan ya ce sai dai ba kamar yadda ake zuwa kullum ba a da ɗaliban za su yi.
Ya ce gwamnati ta tsara cewa ƴara ƴan makarantan firamaren aji 1 da na aji 2 za su rika zuwa makaranta ne a ranakun Litini da Talata kawai.
Sai kuma Ƴan aji 3, 4 da 5 za su rika zuwa a ranakun Laraba, Alhamis da Juma’a.
Su kuma wadanda za su shiga aji daya na karamar sakandare da aji daya na babban sakandare wato JSS 1 da SSS 1 za su yi jiran makonni 5 a gida har sai anngama zangon karatu da ya rage na sauran ajujuwan da suka saura.
Amma kuma ɗaliban ajujuwan JSS 2 da JSS 3 da kuma SSS 2 duk za su dawo karatu kamar sauran.
Haka suma makarantun Islamiya dake fadin jihar duk zasu koma karatu, amma kuma za su kiyaye sharuddan Korona da gwamnati ta saka.
Idan ba a manta gwamnati ta garkame makarantun kasar nan kaf tun a watan Maris a dalilin barkewar annobar Korona Bairos.
Sai dai kuma a cikin watan Satumba gwamnatocin jihohi suka fara sanar da bude makarantu domin yara su koma makaranta.
Jihar Kwara da, Osun da Legas duk sun sanar da bude makarantu n gwamnati da masu zaman kansu.