SARS na da muhimmancin gaske a kasar nan Mu a zamfara mun san da haka kuma ina tare da su – Matawalle

0

Duk da koke-koke da ake yi kafin Buhari ya rusa rundunar SARS, gwamnan Zamfara Bello Matawalle, ya soki wannan zanga-zanga cewa ba alheri bane a gare mu.

Kakakin Gwamnatin jihar Zailani Bappa a wata takarda da ya fitar a madadin gwamna Matawalle, ya ce gwamnan jihar baya tare da masu yin wannan zanga-zanga.

” Ina goyon bayan a cigaba da aiki da rundunar SARS Dari bisa Dari saboda mu a Zamfara mun san kokarin da suke yi mana a jihar.

” Duk wanda kuka ga baya son SARS, to ina tabbatar maku cewa bashi da gaskiya, ko kuma akwai wani abu na rahin gaskiya da yake yi kuma SARS na takura masa.

” Ina kira ga gwamnatin tarayya kada ta kuskura ta saurari masu wannan zanga-zanga, kada ta rusa SARS.

Sai dai kuma kuka da kiran Matawalle bai isa kunnen gwamnati da wuri ba.

A ranar Lahadi da ran tsaka, Sufeto Janar din ƴan sanda Mohammed Adamu ya sanar da rusa sashen ƴan sanda na SARS wanda Buhari ya umarce shi da yayi.

Sai dai kuma tun bayan rusa rundunar, mutane da dama ke tofa albarkacin bakin su game da haka. Da yawa sun ce basu ji dadin rusa wannan sashe na ƴan sanda ba.

Sai dai kuma ba a nan kizo ke sakar ba domin ai ba sallamar jami’an za a yi ba, suna nan a matsayin su na ƴan sandan kasa.

Share.

game da Author