Hadaddiyar Kungiyar fastoci da mabiyan darikar Katolika sun bayyana nuna goyon bayan su ga zanga-zangar #EndSARS da ke gudana a wasu sassan kasar nan.
Kungiyar ta ce ta na tare da masu wannan zanga-zanga na #EndSARS 100 bisa 100, domin ba kawai kawo karshen ta’addancin da ‘yan sanda ke yi bane suke kira da a duba, har da matsalolin da Najeriya ta samu kanta a ciki.
” Muna ganin gwamnati bata fahimci abinda wadannan matasa masu #EndSARS ke nema daga gareta bane da abinda suke so kuma suke kuka akai, ko kuma tsananin dodewar kwakwalwace kawai na irin wannan gwamnati.
” Sannan kuma kawai wai cikin gaggawa wai ta kafa wata rundunar. Matasa masu zanga-zanga suna kan turbar gaskiya akan abin da suke yi yanzu. Muna kira ga gwamnati su koma su yi karatun tanatsu domin muma muna tare da wadannan matasa.
Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin kakakin kunfiyar fastocin Cocin katolika, Augustine Akubeze ranar Asabar.
Idan ba a manta ba a makon da ya gabata, Babban Faston Cocin Redeem RCCG, David Oyedepo ya bayyana goyon bayan sa ga Zanga-zangar #EndSARS da ke gudana a fadin kasar nan a yanzu.
Dubban matasa a fadin kasar nan na yin zanga-zangar #EndSARS a musamman jihohin yankin kudancin Najeriya da Abuja.
A kullum sai sun datse manyan tituna da kasuwannin a jihohin da zanga-zangar ta yi tsanani.
Sai dai kuma gwamnati ta saurari korafin matasan, ta rushe rundunar SARS din amma bai hana su cigaba da zanga-zangar ba.
Oyedepo ya ce dama can ya taba yi wa gwamnati gargaɗin haka tun a 2015.
” Na ja wa gwamnati kunne tun a 2015, cewa na hango bala’i da kata’i da zai kunno kai a kasar nan, kuma na yi ta yi mata gargaɗi amma an yi min kunnen-uwar-shegu. Najeriya bata taba fadawa yanayi irin haka ba da ake kashe-kashen rayuka babu kakkautawa irin shekaru biyar da suka wuce.
” Duk wata tsari na gwamnati da bata damu da yadda ake kashe-kashen rayukan mutanen ta ba, bata da amfani kwata-kwata. A dalilin haka matasa suka fusata yanzu.
Sai dai kuma abinda ya bambamta shine a yankin Arewacin Najeriya kaf, babu jiha daya da ta ke goyon bayan wannan zanga-zanga.
A jihar Barno ma kira suka yi da gaba daya kaf an turo musu ƴan SARS dinne jihar.
Har a kasashen waje ana yin wannan zanga-zanga na #EndSARS.