#EndSARS: Direbobin tankokin motoci sun datse babban titin Yola zuwa Jalingo

0

A daidai lokacin da ake zazzafar zanga-zangar kin jinin SARS a fadin kasar nan har da kasashen waje, a ranar Lahadi kuma Direbobin Mota samfurin tanka, sun datse babban titin da ya tashi daga Yola zuwa Jalingo.

Wani jami’an dan sanda ne ya dirka wa direban tanka bingiga, ya mutu nan take, saboda tankiyar cin hancin naira 400.

Manyan jami’an Kungiyar Direbobin Tanka sun ce ” an bindige masu abokan aikin mu ne, yayin da ‘yan sandan Kerewa Area Command na Kerawa suka tare direban ya na dauke da fetur.”

Shugaban direbobin Muhammad Ali, ya bada hakurin jinkirin da dubban jama’a su ka shiga.

‘Yan sandan Karewa da su ka yi kaurin suna wajen karbar cin hanci, su ne su ka bindige shi, saboda karbar cin hanci

“Lokacin da su ka nemi kudi a wajen sa ba su samu ba, sai su ka yi ta lakada masa dukan tsiya.”

“Wasu mutane masu kishi da tausayi sun ce e shi, su ka garzaya da da shi asibiri.”

Wani direban da abin ya faru a idon sa, ya ce gaskiya sun gaji da yadda ‘yan sanda ke zaluntar su da ‘yan sanda ke yi, ba dare ba rana.

Ana ci gaba da zanga-zanga a fadin kasar nan duk da cewa an eushe SARS.

Sai dai masu zanga-zangar a yanzu na neman a biya diyyoyin dukkan wadanda SARS su ka kashe ko su ka lahanta.

Direbobin manya da kananan motocin da ke bin hanyar Jalingo zuwa Yola, su day masu motocin da ba na haya na hanyarJalingo a yau Lahadi sun dandana kudar azabar da su ka sha. Saboda sun dade a wurin.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Adamawa ya tabbatar da cewa za a yi bincike kuma za a hukunta su.

Share.

game da Author