Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 133 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Lahadi.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Lahadi sun nuna cewa jihar Legas ta samu karin mutum –90, Rivers-13, FCT-8, Kaduna-8, Oyo-6, Ondo-3, Katsina-2, Nasarawa-2 da Filato-1
Yanzu mutum 61,440 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 56,611 sun warke, 1,125 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 3,627 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 20,555, FCT –5,910, Oyo – 3,409, Edo –2,643, Delta –1,812, Rivers 2,696, Kano –1,741, Ogun – 1,980, Kaduna –2,550, Katsina -902, Ondo –1,654, Borno –745, Gombe – 883, Bauchi – 710, Ebonyi –1,049, Filato -3,580, Enugu – 1,313, Abia – 898, Imo – 589 , Jigawa – 325, Kwara – 1,050, Bayelsa – 403, Nasarawa – 476, Osun –908, Sokoto – 162, Niger – 117, Akwa Ibom – 295, Benue – 484, Adamawa – 254, Anambra – 275, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 79, Ekiti – 329, Taraba- 109, Kogi – 5, da Cross Rivers – 87.
Kwamitin PTF ta ce za a ci gaba da garƙame wuraren holewa da gidajen Casu har zuwa wani lokaci.
A ranar Alhamis ne kwamitin Shugaban kan Korona PTF ta shaida cewa baza a bude wuraren shakatawa da kulob ba saboda akai yiwuwar idan a ka bude su za a samu karuwar yaduwar Korona a kasar nan.
Kodinatan kwamitin Sani Aliyu ya sanar da haka a ganawa da kwamitin ta yi da manema labarai a Abuja.
“Ba wai kwamitin bata so a bude ire-iren wadannan wurare bane, tsarin su bai yi kama da inda za a kiyaye dokokin Korona ba.
“A dalilin haka muke bai wa masu zuwa holewa a wurare irin haka da su kara hakuri har sai gwamnati ta gamsu da tsarin wuraren kafin ta bude su.
Shima sakataren gwamnati tarayya kuma shugaban kwamitin PTF Boss Mustapha ya tabbatar da haka yana mai cewa a wurare irin haka babu yadda za a yi a iya kiyaye dokokin Korona.
Mustapha ya ce Idan aka kara hakuri zuwa dan wani lokaci kadan komai zai koma yadda ya ke a da.
Ya ce daukan wannan matakin ya Zama dole ganin cewa babu tabbacin samun maganin rigakafin cutar a kasar nan nan da watanni shida masu zuwa.
Sakamakon binciken NCDC ya nuna cewa Najeriya ta fara samun nasara wajen rage yaduwar cutar korona a kasar Nan.
Binciken ya nuna cewa makonni hudu da Suka gabata adadin yawan mutanen dake kamuwa da cutar basu dara 300.
Sai dai duk da nasarorin da ake samu kwamitin PTF ta koka cewa jihohi 26 basu yi wa mutane gwajin cutar yadda ya kamata a kasar nan.
Hakan kuwa na kara ingiza mutane wajen rashin amincewar da cutar a kasar nan.
A dalilin haka kwamitin ya yi Kira ga mutane da su ci gaba da kiyaye dokokin Korona a ko-ina suke.
Discussion about this post