RASHIN TSARO: Boko Haram sun kashe wani Kanar a Sojojin Najeriya

0

A ci gaba da munin hare-haren da Boko Haram ke kaiwa, sun kashe wani babban sojan Najeriya mai mukamin Kanar a Damboa, Jihar Barno.

PREMIUM TIMES ta tabbatar da kisan babban sojan, kuma ta boye sunan sa, saboda har yanzu babu tabbacin ko Hukumar Sojoji sun sanar wa iyalan sa, ko ba su sanar masu ba.

Kanar din kuma Birgade Kwamanda ne na wata Rundunar soja, a Damboa, Jihar Barno inda sojoji ke gumurzun yaki da Boko Haram.

PREMIUM TIMES ta ji daga majiya cewa Boko Haram kwanton-bauna su ka yi wa motar da sojan ke ciki tare da wasu sojoji kusa da Damboa.

Garin Damboa na tazarar kilomita 85 daga Maiduguri.

Har yanzu dai babu cikakken bayanin yadda aka kai masu harin. Amma majiya ta ce za a rufe gawar babban sojan a ranar Talata.

An tambayi kakakin Sojojin Najeriya, Sagir Musa. Sai dai bai ce komai game da kisan da aka yi wa Kanar din ba.

Ya dai ce za su fitar da sanarwa ga ‘yan jarida akan wani haki da aka kai a Barno.

Share.

game da Author