Ranar Lahadi ne Babban Basaraken kabilar Yarabawa, Ooni na Ife, Adeyeye Ogunwusi, Ojaja II, ya hau cikin Fadar sa ta Ile Mole, Iremo da ke kan tsauni a Ile-Ife, inda zai shafe kwanaki 7 domin fara gagarimin bukin kabilar Yarabawa na Olojo.
Kafin fitar ta sa, ya yi shiga ta fararen kayan gargajiya, yayin da ya ke fita daga kasaitacciyar Fadar sa ta Oodua da ke Ife.
Ya shaida wa manema labarai cewa yanzu lokacin neman kusantaka da ubanjigi ne tare da yin addu’ar neman rabuwa da cutar Korona baki daya.
Ya ce addu’ar ta kuma hada har da na neman zaman lafiya da yalwar arziki a fadin Najeriya.
Oba Ogunwusi ya yi bayanin cewa bukin Olojo bukin ibada ne wadda ke kara kusanta mutum da ubangiji.
“Zan tafi na kebanta kai na da jama’a kwanaki bakwai, ina mai azumi da addu’o’i ga kakannin-kakannin mu.
“Idan na kammala kwanaki bakwai bisa tsauni na sauko, to su kan su allolin mu akwai gagarimar tankiya a tsakanin su. Saboda Aare shi ne ya fara sarauta.
“Akwai lokacin da wadannan alloli su ka taru baki dayan su a Ita Oranfe, su ka amince cewa to dan Adam tsari na shugabanci. Ai daga nan ne mulki na zamanin da ake ciki yanzu na dimokradiyya ya wanzu, har ma da sauran salon gwamnatoci daban-daban ” Inji babban basaraken na Yarabawa.
A wadannan kwanaki bakwai da zai yi a kebance, ba zai ga kowa ba, babu wanda zai kuskura ya gan shi. Ba zai gana da kowa ba.