Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 162 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Asabar.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Asabar sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum -53, Gombe-21, Oyo-19, Delta-12, Ondo-11, Filato-10, Ebonyi-9, FCT-6, Kwara-6, Kaduna-5, Rivers-3, Ogun-2, Anambra-2, Imo-2 da Ekiti-1
Yanzu mutum 54,905 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 42,922 sun warke, 1,054 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 10,929 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 18,308 , FCT –5,279, Oyo – 3,187, Edo –2,594, Delta –1,768, Rivers 2,175, Kano –1,727, Ogun – 1,678, Kaduna –2,189, Katsina –812, Ondo –1,561, Borno –741, Gombe – 744, Bauchi – 669, Ebonyi – 1,014, Filato -2,720, Enugu –1,184, Abia – 807, Imo – 534, Jigawa – 322, Kwara – 982, Bayelsa – 391, Nasarawa – 437, Osun – 795, Sokoto – 159, Niger – 244, Akwa Ibom – 280, Benue – 460, Adamawa – 228, Anambra – 221, Kebbi – 93, Zamfara – 78, Yobe – 67, Ekiti – 282, Taraba- 87, Kogi – 5, da Cross Rivers – 83.
Maganin rigakafin Korona zai kai tsakiyar shekarar 2021 – WHO
Hukumar kiwon Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa duk da cewa wasu kasashen duniya na fidda wasu magunguna na rigakafin cutar Korona, za a kai tsakiyar shekarar 2021 kafin a samu wanda aka tabbatar da ingancin sa.
Mai magana da yawun hukumar Margaret Harris, ta bayyana cewa hukumar bata amince da ingancin wadannan magunguna ba tukunna dukkan su sunananan a matakin gwaji.
Sai dai kuma tuni har kasar Rasha ta ce ta gama hada maganin rigakafin cutar har kuma ma ta fara amfani dashi.
Najeriya ta karbi samfurin wannan magani na rigakafi.
Ministan Kiwon Lafiya, Osagie Ehinare ya bayyana cewa an aika da wannan magani ma’aikatar NAFDAC domin cigaba da aiki a kai.
Discussion about this post