CIGABA YAZO: Yadda Bafulatana mai tallan Nono ke dama Fura da Na’urar Markade

0

Idan da za a ce maka akwai ranar da za a wayi gari bafulatana mai tallan Nono za ta rika yawon talla da Na’urar markade ‘Blender’ domin dama fura da nono zaka iya yin musu. Yanzu cigaba ya kawo mu wannan lokaci.

Bafulatana dauke da kwaryar ta na Nonon ko roba, ta zauna a wurin saida fura, idan Kazo sai ta dibi nono da saka fura maimakon ka gani a kwarya sai kawai kaga ta saka maka cikin na’urar markade da ake kira blender da turanci ta makala shi a wuta ta dama maka wannan fura.

Haka wakilin PREMIUM TIMES HAUSA ya hango haka a Kaduna, inda ya iske dandazon matasa a kan layi na tsaitsaye wajen wata bafulatana dama musu fura da Nono da wannan inji.

Irin wannan sana’a na dama fura da Nono ba sabon abu bane saidai ya zama sabo ga wasu da dama har da wakilin PREMIUM TIMES wanda hakan shine karon sa na farko da ya ga mace bafulatana a wajen sana’arta tsugune tana jona wannan na’ura tana dama fura da shi maimakon Kwarya da Ludayi.

Wannan mata dai ta ce hakan yana mata sauki kuma ya na sa ta iya biya wa dandazon masu bukatar fura cikin dan kankanin lokaci.

Idan dai dama furar za a yi da kwarya, za a iya daukan minti 2-3 amma da wannan na’ura, cikin minti sakan 30 ka sallami mutum.

Duk da cewa shaguna da dama tuni sun karbi wannan sana’a ta saida fura da nono hannu bibiyu, wato su hada da yogot ko madara su dama da blender, wasu da yawa sun fi jin dadin su sha wanda aka dama da cikin kwarya kumai dadewan da za a yi.

Share.

game da Author