Yadda sojojin saman Najeriya suka darkake yan ta’adda a dazukan Kaduna

0

A cigaba da fatattakar ‘yan ta’adda da kawo karshen hare-hare da ke yi a kauyuka da dazukan dake kewaye da dazukan jihar Kaduna, rundunar sojojin Saman Najeriya sun afka wannan dazuka inda suka yi ta luguden wuta daga sama babu kakkautawa.

Wannan farmaki da jiragen yakin suka kai sun dirawwa dazukan Kudaru da Kuyambana wanda yayi ajalin ‘yan ta’adda da dama dake boye a wannan dazuka sannan kuma ragargaza sansanonin su.

Hedikwatar tsaron Najeriyar ta ce za a cigaba da kai irin wadannan hare hare har sai an kawo karshen ta’addancin da ‘yan ta’adda ke aikatawa a yankunan jihar baki daya.

Idan ba a manata ba an ruwaito yadda Sojojin Kasa suka darkaki maboyan ‘yan ta’adda, inda suka kashe wasu hudu da dukkan su masu garkuwa da Mutane ne.

Baya ga yabawa wadanda dakarun Najeriya bisa wannan aiki da suka yi na darkake wadannan muggan mutane da suka addabi mutanen jihar, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ta yaba da wannan nasara da dakarun Najeriya suka samu akan ‘yan ta’adda.

Bayan haka Kwamishina Aruwan ya kara da yin kira ga mutane da su daina alakanta ta’addancin da ke faruwa a jihar da Kabilanci ko addini, sannan ya ce gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna El-Rufai, a aiki tukuru don ganin an kawo karshen wannan ta’addanci.

Share.

game da Author