1 – Iya Bashar Aminu
Iya Bashir dan sarkin Zazzau Aminu ne wanda marigayi Shehu Idris ya gada bayan ya rasu. Shine hakimin Sabon Garin Zazzau. An haifi Iya Bashar ranar 26 ga watan Disambar 1960. Ya rike mukaman gwamnati da dama bayan kammala karatun sa.
Iya ya fito daga gidan Katsinawa ne.
2 – Yerima Mannir Jaafaru
Mannir Jaafaru Yeriman Zazzau, Shi kuma ya fito ne daga gidan Bare-bari. Shima kasaitaccen basarake ne a yankin Zariya sannan ma’aikaci ne. Yayi karatu a kasa Najeriya da kasashen waje sannan kuma ya rike mukamai da dama a Najeriya.
3 – Magajin Gari Ahmed Bamalli
Ahmed Bamalli ne jakadan Najeriya a kasar Thailand, yanzu ya koma Myanmar. Yayi karatun Boko a Najeriya da kasashen waje.
Ahmed Bamalli ya fito daga gidan Mallawa kuma shine Magajin Garin Zazzau.
4 – Aminu Idris
Aminu Idris Turakin Zazzau, shine babban dan sarkin Zazzau mai rasuwa, Shehu Idris. Yana aikin a kamfanin Mai na kasa. Ya auri Karimatu ‘yar Iya Bashar Aminu da shima yana neman sarautar Zazzau din.