Ko ka san yawan wanka da ruwan zafi na rage karfin maniyin namiji? – Gargadin Likita

0

Wani Likita mai suna Peter Atangwho ya yi kira ga maza da su rage yawan wanka da ruwan zafi cewa yawaita amfani da shi na rage karfin maniyin namiji.

Atangwho wanda ke da asibitin ‘TeleMed Online Clinic’ ya ce wanka da ruwan zafi akai-akai na rage karfin maniyyin namiji da kan hana sa ya iya yi wa mace ciki.

Sai dai likitan ya ce ba wai a daina kwata-kwata bane , amma rage yin haka na da matukar amfani domin samun lafiya.

Ya kara da cewa shi ‘ya’yan maraina saboda ana so ya kasance a wuri da zai zamo cikin sanyi yasa Allah ya halicce shi a can kasa tsakanin kafafuwa.

Ya bada shawarwari kamar haka ” Yana da kyau mutum ya rika kwana babu wando sannan a rika saka kamfai mai alawus maimakon irin wanda ke matse jiki kafin a saka wando idan za a fita.

Hanyoyin dake rage karfin maniyin namiji

1. Kiba

2. Shan taba ko wiwi.

3. Yawaita shan giya.

4. Yawan wanka da ruwan zafi.

5. Cin abincin da aka soya ko Kuma suke kara kiba a jiki.

6. Yawan saka matsatsen wando.

7. Kamuwa da cutar sanyi.

8. Ta’ammali da miyagun kwayoyyi.

9. Yawan damuwa.

10. Cin abincin dake dauke da sinadarin ‘Caffeine’.

Hanyoyin karfafa maniyin namiji.

1. Motsa jiki.

2. A guji cin abincin dake Kara kiba a jiki.

3. Yawaita cin ganyayakin

4. Rage yawan amfani da ruwan zafi.

5. Rage damuwa.

6. A Rika cin dabino da kwakwa.

7. A Rika cin kifi.

8. A sauna saka wandon da ya matsi namiji musamman Idan za a kwanta barci.

9. A yawaita shan ruwa ba sai ana jin kshi ba.

10. Nisanta Kai da na’urorin dake da zafi musamman a gaban namiji.

Share.

game da Author