Gwamna Nasiru El-Rufai na Jihar Kaduna ya sa hannu kan Dokar Jihar Kaduna ta 2000, wadda aka yi wa kwaskwarimar hukuncin wanda ya yi wa kananan yara fyade.
Kakakin Gwamnan Kaduna, Muyiwa Adekeye ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
Sabuwar dokar tanadar da dandake golayen namijin da ya yi lalata da kananan yara da kuma kassara macen al’aurar macen da ta yi fyaden kananan yara. Haka kuma akwai wuraren da dokar ta tanadi hukuncin kisa.
Bayan haka kuma, wadanda kotu ta yanke wa hukuncin za a rattaba sunayen su a Rajistar Masu Lalata Kananan Yara a Ofishin Antoni Janar na jihar da abin ya faru.
Tuni dai dokar ta fara amfani tun daga ranar 11 Ga Satumba, ranar da El-Rufai ya sa wa dokar hannu.
Dokar ta tanadi tsatstsauran hukunci fiye da hukuncin baya na daurin shekara 21 ga wanda ya yi wa baliga fyade, kuma daurin rai-da-rai ga wanda ya yi wa karamar yarinya fyade.
A karkashin wannan sabuwar doka, hukuncin wanda ya yi wa ‘yar kasa da shekara 14 ko dan kasa da shekara 14 fyade, to za a dandake masa golaye ne, ta yadda zai daina sha’awar mace kwata-kwata a rayuwar sa. Amma ba za a kashe shi ba.
Idan karamin yaro ne ya yi fyaden, to za a yi masa hukunci daidai da wanda dokar hukunta kananan yara ta 26 ta shekarar 1991 ta Jihar Kaduna ta tanadar.
Yayin da ya ke jinjina wa ‘Yan Majalisar Jihar Kaduna saboda amincewa da wannnan doka da suka yi.
Gwamnan ya ce akwai matukar bukatar kafa dokar, domin ta haka ne za kawar da laifukan cin zarafin kananan yara.
Ga Yadda Dokar Ta Ke Dalla-dalla:
1. Duk baligin da ya yi wa yaro ko yarinya ‘yan kasa da shekaru 14 fyade, to hukuncin sa a dandake masa golaye, sannan a kashe shi.
2. Wanda ya yi luwadi da karamin yaron da bai kai shekara 14 ba, to doka ta ce a dandake masa golaye sannan a kashe shi.
3. Inda aka kama mace ta yi wa karamin yaro fyade, to a kassara mata al’aura, sannan a kashe ta.
4. Inda aka yi wa ‘yar sama da shekara 14 fyade, to wanda ya yi fyaden za a dandake golayen sa, sannan ya zauna kurkuku daurin rai-da-rai.
5. Idan karamin yaro ya yi fyade, za a yi masa hukunci daidai yadda Dokar Hukunta Kananan Yara ta 1991, ta Jihar Kaduna ta tanadar.
6. Idan wanda aka yi wa fyaden karamar ysrinyay ce ko karamin yaro, to baya ga hukunci, za a rattaba sunan mai laifin a Rajistar Lalatattun Mutanen Banza Masu Bata Kananan Yara.
Za a ajiye rajistar a Ofishin Antoni Janar domin kowa ya rika sanin lalatattun mutanen.
7. Idan kotu na shari’ar da ta danganci yi wa kananan yara fyade, to akwai bukatar a samu rahoton likita ko likitocin da su ka duba su ka tabbatar an aikata fyaden.