Dalilin da ya sa kotu ta yanke wa barawon dawa hukuncin bulala da tara a Jigawa

0

Kotun Shari’a dake Dutse a jihar Jigawa ta yanke wa wani barawo da ya saci tiya tara na dawa hukuncin bulala biyar.

Kotun wace ta yi amfani da dokar penal code ta bai wa Abdullahi Ya’u mai Shekarau 20 zabi ya biya taran Naira 3000 ko ya yi zaman gidan yari na wata biyar.

Alkalin kotun Muhammed Adamu ya ce kotu ta yanke wannan hukunci ne domin ya zama ishara ga wasu da ke da irin wannan hali.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta Kama YA’u a ranar Talata da ya gabata sannan a wanna rana kotu ta yanke Masa hukunci.

Kafin a yi wa Ya’u bulala lauyan da ya shigar da karar ya tambayi Ya’u ko ya gamsu da hukunci da kotu ta yanke masa ko kuma zai daukaka Kara zuwa babban kotu.

Ya’u ya ce ya gamsu sannan ya durkusar wani jami’in kotun ya tsatsaula masa bulala da biyar sannan nan take ya biya kudin belin sa, naira 3000.

Share.

game da Author