SOKE GAYYATAR EL-RUFAI: Siyasa da son kai ne ya ingiza NBA fadawa cikin wannan Cakwakiya – Kungiyar Lauyoyi Musulmai ta Kasa

0

Kungiyar Lauyoyi Musulmai ta Kasa, ta bayyana cewa bincike da ta gudanar kan dalilin da ya sa uwar Kungiyar NBA ta soke gayyatar da ta yi gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, sun gano cewa wasu ‘Yan siyasa ne suka hada baki da wasu tsirarun ‘yan kungiyar domin su ci mutuncin gwamna El-Rufai saboda wata banbancin ra’ayi na siyasa.

Shugaban MULAN na kasa Farfesa Abdulqadir Abikan da sakataren kungiyar Ibrahim Alasa sun bayyana cewa kungiyar NBA ta jefa kanta cikin cakwakiyar siyasa da ta biye wa wasu da ke so su cimma burin su maimakon tsaya wa akan turbar gaskiya da kare mutuncin kungiyar.

” Idan har saboda wadannan dalilai ne da kungiyar ta bayyana wai sune suka sa ta dakatar da El-Rufai, ashe duk wanda ya taba aikata abu mai kama da abinda suke zarginsa dashi bai kamata a barshi ya yi jawabi a taron kungiyar ba.

MULAN ta kara da cewa uwar kungiyar ta yi gaggawar soke gayyatar gwamnan ba tare da ta yi nazarin dalilan da masu korafi suka fadi ba da kuma baiwa gwamnan daman kare kansa ba.

A karshe kungiyar ta ce abinda ya fi dacewa kungiyar NBA ta yi yanzu shine, ta soke sashen da aka saka dama El-Rufai zai yi magana sannan ta janye gayyatar duk wani wanda yake da guntun kashi a duwawun sa na wani abu da ya taba aikatawa da yayi kama da abinda ake zargin shine dalilin da ya sa aka soke gayyatar El-Rufai.

“Wadannan shawarwari sune dole kungiyar za ta warware su cikin gaggawa idan ta na so wannan taro yayi tasiri a bana.” Inji MULAN

Share.

game da Author