Yadda ‘Yan bindiga suka sace dalibai masu shirin rubuta jarabawa da malamar su a Kaduna

0

Mahara akan babura dauke da bindigogi sun afka wani makarantar sakandare a daidai dalibai na daukan darasi a ajujuwan su a karamar hukumar Chikum, dake jihar Kaduna.

Maharan sun tarwatsa dalibai da malaman su sannan suka sace wasu dalibai bakwai da malamar su daya.

Wannan hari ya auku ne ranar Litinin da misalin karfe 8 na safe a kauyen Damba-Kasaya, dake karamar hukumar Chikum.

Wani mazaunin kauyen Akila Barde da ya tattauna da wakilin PREMIUM TIMES, ya shaida mana cewa maharan sun dira kauyen tun da sanyin safiyar Litini ne.

” Maharan sun shigo wannan kauye ne a kan babura dauke da makamai suna ta harbe-harbe, daga nan sai suka zarce makarantar Prince Academy. Sun dauke dalibai 7 da malamar su daya mai suna Christiana Madugu.

” Haka kuma maharan sun kashe wani mazaunin kusa da makarantar mai suna Benjamin Auta.

Bayan haka Akila ya ce, matasan gari sun fafuri wadannan mahara da yasa suka saki wasu ‘yan gari da suka yi garkuwa dasu a lokacin da suke gudu dasu cikin kungurmin daji.

Sannan kuma sun ciccinna wa wasu gidaje a kauyen wuta kafin su fice.

Kakakin ‘Yan sandan jihar, da kwamishinan Tsaro duk basu ce komai a kai ba tukunna.

Jihar Kaduna na daga cikin jihohin da hare-haren ‘yan bindiga yayi kamari a yankin Arewa.

A rahoton wani bincike da aka fitar, jihar ce ke kan gaba wajen yawan wadanda suka rasu a dalilin hare-haren mahara a watan Yuli.

Daga Kaduna sai Zamfara da Katsina.

Share.

game da Author