RASHIN TSARO: A bari kowa ya mallaki bindiga kawai – Gwamna Ortom

0

Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai ya nemi Gwamnatin Tarayya ta kyale kowane dan Najeriya ya mallaki bindiga domin kare kan sa daga matsalar rashin tsaron da ke damun kasar nan.

Ortom ya yi wannan kira a wurin taron cika shekara daya da sake kafa Ma’aikatar Kula Da Harkokin ‘Yan Sanda.

A wurin taron, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Muhammad Adamu ya yi dogon bayanin yadda za a kashe naira bilyan 13.5 da Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a kashe wajen kafa jami’an tsaron kula da unguwanni, wato ‘Community Police’.

A jawabin na sa, Ortom ya ce, “ya zama tilas duk mu tashi tsaye, mu yi da gaske, kafin matsalar rashin tsaro ta durkusar da kasar nan.”

“Na ji mutane na ta korafi da gunaguni don kawai saboda Ortom ya ce a bar ‘yan Najeriya su mallaki bindiga domin kare kai. Wai a cewar su, idan kowa ya mallaki bindiga, to za ta dagule gaba daya.

“To su kuma makiyayan da ke yawo da bindiga AK 47 fa, su na yin garkuwa da mutanen da ba su ji ba, kuma ba su gani ba. Su na Kama matayen mu su na yi musu fyade, su kona garuruwan mu da kauyukan mu, su na yi mana ta’addanci?

“Shin me ya sa ba za mu iya kwace wadannan bindigogi daga hannun su ba? Guda nawa aka kama a cikin su?” Tambayoyin da Ortom ya yi kenan a wurin taro, a gaban Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya.

Ya ce an yi biris da shawarar da ya bayar, amma sai yawan kama masu garkuwa ake yi dauke da bindiga kirar AK-47.

“Ni shawarar da na ke son bai wa Gwamnatin Tarayya ke nan. A Amerika ana bai wa mutane lasisin mallakar bindiga, kuma rayuwa na tafiya bakin gwargwado. Hakan bai sa kasar ta dagule ba.

“Amma dai ni har yanzu ina nan kan ra’ayin cewa a bai wa ‘yan Najeriya damar mallakar bindiga.”

Ya ce jami’an tsaro a Jihar Benuwai sun kama makiyaya sama da 400, wadanda suka karya dokar hana kiwo a jihar.

“Akasarin wadanda aka kama din nan kuma duk Fulani ne, an kuma gurfanar da su a kotu. An yanke wa 130 hukunci a kotu. Wasu hukuncin dauri ko tara, wasu kuma hukuncin tara. Sun kuma biya.

“Mun kuma kama shanu sun kai 9000. Amma kamar yadda doka ta tanadar, idan an kama shanun ka za ka biya tara. Idan ka biya tara kuma, ba a yarda ka kora shanun ka ka shiga daji da su ba. Sai dai ka samo mota ta daukar maka su, ka kara gaba.” Inji Gwamna Ortom.

PREMIUM TIMES ta tuntubi Kakakin Yada Labarai na Gwamna Ortom, inda a ranar Asabar ya yi karin bayanin cewa, “Gwamna ya na nufin sai mutumin kwarai za a bari ya mallaki bindiga, ba kowane tarkace za a bari ya mallake ta ba.”

Share.

game da Author