Yadda jirgin sama ya kusa rikitowa kasa da mu – Aisha Buhari

0

Uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari ta bayyana yadda ita da sauran ‘yan rakiyar ta suka tsallake rijiya da baya, lokacin da jirgin sama ya kusa rikitowa kasa da su, kan hanyar dawowar su daga Dubai.

Aisha ta ce ta yi tafiya ne zuwa Dubai domin duba lafiyar ta, kuma ta dawo a cikin Jirgin Sojojin Yakin Saman Najeriya.

“A kan hanyar dawowar mu Najeriya ne, sai jirgin mallakar ‘Nigerian Airforce Flight’ ya shiga cikin gajimarai masu karfi sai jirgin ya rika gargagada da jijjiga mai karfi. Amma a haka matukan jirgin suka fita cikin gargada da jijjigar nan a cikin yanayin nuna kwarewa da bajinta.”

Haka Aisha ta bayyana a shafin ta na Twitter da yammaci bayan ta dawo Najeriya.

Ba a san irin ciwo ki rashin lafiyar da Aisha Buhari ta fita neman wa magani a Dubai ba.

Amma dai ta bayyana cewa yanzu ta murmure sosai, kuma ta wartsake, kuma ta dawo Najeriya.

Aisha ta kara jinjina wa kwarewar matukan jirgin tare da nuna gamsuwa da yadda ake kula da yi wa jiragen garambawul da gyare-gyare kan kari.

“Ba matukan jirgin kadai zan yi wa jinjina ba, har ma da sauran Sojojin Saman Najeriya baki daya, saboda irin jajircewar da suke nunawa wajen tafiyar da aikin su, da kuma yadda suke kula da jiragen saman da ke hannun su.” Haka ta rubuta bayan ta tsallake rijiya da baya.

Dama dai tun da Shugaba Buhari ya hau mulki, shi da dukkan iyalan sa su na fita kasar waje ne ganin likita.

Alkawarin da ya yi na daina fita kasar waje a duba lafiyar sa idan ya hau mulki, har yau dai bai cika shi ba. Hasali ma iyalan sa da wasu makusantan sa ma ba su daina zuwa waje neman magani ba.

A zangon sa na farko, Buhari ya sha fita waje ganin likita, duba lafiya da kuma jiyyar da ya yi wata da watanni bai dawo ba.

Sau da yawa ‘yan Najeriya na nuna rashin jin dadin irin makudan kudaden da ake kashewa wajen fitar da Buhari ko iyalan sa je yi zuwa waje. Hakan ne ya sa ake yawan matsa wa shugabanni lamba cewa babu wani uzurin da za su bayar na kasa inganta asibitocin Najeriya.

Aisha ta nemi a inganta asibitocin Najeriya kuma ta nemi a gaggauta amfani da tsarin tallafin lafiya na Bankin CBN na naira bilyan 100 domin da bankin ya fitar da matakan samarwa tun a ranar 25 Ga Maris, 2020. Ta ce za a iya kaiwa ga talllafin ta bankin ‘yan kasuwa daban-daban na kasar nan.

Share.

game da Author