Manoman masara na jihar Kaduna sun koka kan rashin isowar kayan tallafin noma na ‘ABP’ a kan lokaci

0

Kungiyar manoma, masu sarrafawa da siyar da masara (MAGPMAN) dake karkashin Shirin ‘Anchor Borrowers Program’ reshen jihar Kaduna sun koka da rashi samun kayan tallafin kayan noma da shirin tare da hadin gwiwar bankin ‘EcoBank’ ta yi alkawarin rabawa namoman jihar.

Kungiyar MAGPMAN sun bayyana haka ne a zaman da kungiyar ta yi da wakilan shirin ‘Anchor Borrowers Program’ da bankin ‘EcoBank’ a Zaria ranar Alhamis.

Idan ba a manta ba a ranar 29 ga Yuni MAGPAMAN ta raba wa manoman kungiyar 3,535 kayan noma da aka kiyasta kudin su zai kai naira 644.99 a jihar Kaduna.

Shugaban kungiyar Lawal-Maishanu Gazara ya ce an shirya taron ne domin magance matsalolin da manoman masara dake karkashin kungiyar ke fama da su.

Gazara ya koka kan yadda kungiyar ta kasa Samar wa manoman kayan noma musamman takin zamani da buhunan da za a zuba masara bayan girbi kan lokaci.

Gazara ya ce kungiyar ta ware kudade domin rabawa wa manoma da za su yi amfani da su wajen biyan masu musu aiki a gona amma har har yanzu ba a basu ba.

Ya yi kira ga masu ruwa da tsaki dake da baki a kungiyar da su taimaka domin a samu nasara akan abinda aka saka a gaba. Sanna kuma tuni har an fara rabawa manoma kayan noma na badi.

Ya Kuma ce kungiyar za ta hada hannu da hukumar kula da aiyukkan noma na jihar Kaduna domin samar da dabarun aiyyukan noma na zamani.

Share.

game da Author