Shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya Samson Ayokunle ya yi kira ga gwamnatin Kaduna da ta maida hankali matuka wajen kawo karshen rashin zaman lafiya da ya adabaibaye yankin Kudancin Kaduna.
Ayokunle ya bayyana cewa wannan ziyara da ya kawo Kaduna na da mahimmanci matuka ganin cewa wannan rikici da kashe-kashe ya ki ci yaki cinyewa.
” Wai shin wadannan mahara aljanu ne da ba a ganin su? Ko ko shi kenan idan aka kai hari ba za a sake jin ko an kama wani ba ko kuma an hukunta kowa ba. Sai ace ana farautar su kullum.
” Wannan tashin hankali na ci mana tuwo a kwarya domin kashe kashen yayi yawa. muna kira ga gwamnatin Kaduna ta kawo karshen haka domin ita ce hakkin kare mutane, saboda haka lallai ta maida hankali akan haka.
Shi ko gwamna El-Rufai ya bayyana wa tawagar Malaman kiristocin ne cewa tabbas, gwamnatinsa bata na kokarin ganin ta kau da wannan matsala a Kaduna.
” Yadda ake yada labaran Kashe-kashen yana tada mana da hankali matuka domin kusan duka karerayi ne ake yada wa. Sai a rika jingina kashe-kashen da addini, wanda ba haka bane.
” Wannan kashe-kashe bai sake da irin wanda ake yi a Katsina, Zamfara da sauran jihohin da mahara suke addaba ba. Amma na Kaduna da karfin tsiya ake canja yanayin sa, ake malkwada shi dole-dole sai an maida shi addini ko kabbilanci.
” Babu gaskiya a cikin wannan abu kuma mu ba za mu canja salon mulkin mu ba domin mu dadad wa wasu kalilan rai. Abinda ya dace shine za muyi domin Allah zai tambaye mu ranar gobe kiyama.
Itama mataimakiyar gwamnan Kaduna Hadiza Balarabe ta koka ne kan yadda ake lauya maganan rikicin Kaduna sannan da rika fadin abubuwan da ba haka ba.
Shima Kakakin jihar Kaduna, Yusuf Zailani a nashi jawabin ya gargadi malaman addinai ne da su rika fadi wa mabiyan su gaskiyar magana maimakon yin amfani da addini wajen tada zaune tsaye.
Shi ko sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Uba Sani kira yayi ga gwamnati da ta hukunta duk wanda aka kama da hannu a tada zaune tsaye a jihar.