Gwamnatin Tarayya ta jaddada wa jihohi 36 na kasar nan cewa za ta taimaka musu wajen karbo kudaden harajin ladar-ganin-ido (stamp duty) da jama’a suka ki biya tsawon lokaci mai tsawo a baya.
Ministan Harkokin Shari’a Abubakar Malami ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da taron kwamishinonin shari’a na jihohi 36 da shugabannin hukumar karbar haraji na kasa da kuma Shugaban Hukumar Tara Kudaden Haraji ta Kasa tare da Kwamitin Kwato Kudaden Haraji.
Malami ya nemi hadin kan kwamishinonin shari’ar da kuma kwamitin kwato kudaden haraji sakamakon kokarin su na karbo kwantan haraji tun da watan Janairu 2016 zuwa Yuni, 2020.
Ministan ya jawo Sashe na 111 na Dokar ‘Stamp Duty’, wadda ta ce dukkan irin wannan haraji an damka wa Ofishin Akanta Janar na Tarayya ikon karbo basussukan a madadin Gwamnatin Tarayya da ta jihohi.”
Kwanan baya ne Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin Ministoci da zai Tantance da Karbo Basussukan Kudaden Harajin da ya dade ba a biya ba, na ‘stamp duty’.
Makami ne shugaban kwamiti, wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ne ya kafa shi a ranar 30 Ga Yuni.
Mambobin Kwamitin sun hada da wakili Ma’aikatar Harkokin Kudade da Kasafin Kudi da Tsare-tsare, Ofishin Akanta Janar na Tarayya, CBN da sauran su.
An kirkiro harajin ‘stamp duty’ tun a Dokar 1939. Gwamnatin Buhari ce ta sake bijiro da shi.