Hukumar gwamnati ta rufe kamfanin sarrafa man gyada a Abuja

0

Hukumar kula da ingancin abinci ta gwamnati tarayya FCCPC ta rufe kamfanin sarrafa mangyada ‘Apples and Pears’ dake Abuja.

FCCPC ta kama Kamfanin da laifin saidawa da ajiye mangyada da wasu kayan abincin da lokacin aikin su ya kare.

Kayan abincin da lokacin aikin su ya kare sun hada da mangyadan mai suna ‘Laziz vegetable oil, da man salat.

Bayan bincike da hukumar ta yi bisa wasu korafe-korafe da akai mata ta gano tabbas wannan kamfani na saida kayan da lokacin aikin su ya kare sannan kuma ta sarrafa wasu kayan abincin ba bisa ka’ida ba.

Sannan kuma kamfanin da ke aiki a titin Ibadan -Legas bashi da alamar shaidar kamfanin.

Shugaban hukumar Babatunde Irukera ya ce a dalilin haka hukumar ta dakatar da wadannan kamfanoni.

Irukera ya ce za a bude Kamfanin ne bayan hukumar kula da ingancin magunguna da abinci ta kasa NAFDAC ta kammala binciken tabbatar da kayan da kamfanin ke sarafawa da kuma lokutan da za su kare aiki.

A karshe kuma, hukumar ta godewa wadanda suka sanar da ita ayyukan da wannan kamfani ke yi a boye.

Share.

game da Author