Ganin yadda cutar KORONA ke dada yaduwa a kasar nan gwamnati ta ware naira biliyan 8.49 domin siyo kayan yin gwajin cutar a kasar nan.
A jawabin da ministan kiwon lafiya Osagie Ehinare yayi a wajen taron majalisar zartaswa ta Kasa ranar laraba, ya ce hakan ya zama dole ganin yadda cutar ke dada yaduwa a Najeriya.
Ya ce siyo wadannan na’urori zai taimaka wajen aikin dakile yaduwar annobar Korona a duniya.
Osagie ya ce hukumar NCDC za ta bude sabbin wurare yin gwajin Korona a duk kananan hukumomin dake kasar nan domin dakile yaduwar cutar.
Sakamakon gwajin cutar covid-19 da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba ya nuna an samu karin mutum 453 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Laraba.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum – 113, FCT-72, Filato-59, Enugu-55, Kaduna-38, Ondo-32, Osun-26, Ebonyi-20, Ogun-9, Delta-8, Borno-7, Akwa Ibom-6, Oyo-5, Bauchi-1,, Kano-1 da Ekiti-1.
Yanzu mutum 47,743 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 33,943 sun warke, 956 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 13,512 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 16,188 FCT – 4,603, Oyo – 2,900, Edo – 2,399, Delta –1,621, Rivers 1,998, Kano –1,644, Ogun – 1,509, Kaduna – 1,729, Katsina –746, Ondo –1,359 , Borno –697, Gombe – 635, Bauchi – 579, Ebonyi – 967, Filato -1,667, Enugu – 1,069, Abia – 663, Imo – 486, Jigawa – 322, Kwara – 882, Bayelsa – 351, Nasarawa – 371, Osun – 678, Sokoto – 154, Niger – 226, Akwa Ibom – 251, Benue – 430, Adamawa – 199, Anambra – 156, Kebbi – 90, Zamfara – 77, Yobe – 67, Ekiti – 196, Taraba- 78, Kogi – 5, da Cross Rivers – 73.
Discussion about this post