BOKO HARAM: Gwamnonin Arewa na bukatar a binciki zargin gwamnan da aka ce shi ne gogarman Boko Haram

0

Gwamnonin Arewa 19 a karkashin inuwar Kungiyar Gwamnonin Arewa (NGF), ta nemi a yi binciken zargin da tsohon Mataimakin Gwamnan Bankin Najeriya (CBN), Obadia Mailafia ya yi cewa daya daga cikin gwamnonin ne babban kwamandan Boko Haram.

Mailafia wanda kuma ya taba fitowa takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar ADC, ya kara yin zargin cewa, “daya daga cikin gwamnonin Arewa ne kwamandan Boko Haram a Najeriya.”

Ya yi wannan zazzafan ikirari a wata hira da aka yi da shi a gidan Radiyo na Nigeria Info Abuja 95.1FM a ranar Litinin.

Mailafia ya ce wani tubabben dan Boko Haram ne ya shaida masa cewa gwamnan wanda dan Arewa ne ke shugabancin Boko Haram.

Bayan yin wannan ikirari ne jami’an SSS na Kasa suka gayyace shi domin yi masa tambayoyi a ranar Laraba. Sai dai kuma bayan ya shafe awoyi samada shida, an kyale shi ya tafi gida.

Mailafia ya kara da cewa lokacin zaman gida tilas, an rika ganin dandazo da tururuwar ‘yan bindiga su na karakainar jidar muggan makamai a fadin kasar nan.

“Mun gana da wasu daga cikin wanda suka ce sun tubabbu ne. Mun zauna da su ba sau daya ba, suna yi mana bayanin yadda wani gwamnan Arewa ne babban gogarmsn Biko Haram.

Ba Za Mu Yi Watsi Da Wannan Zargi Ba -Gwamninin Arewa

Cikin sanarwar da suka fitar, wadda Daraktan Yada Labarai na Kungiyar Gwamnonin, Makut Simon, Gwamnonin sun ce wannan zargi ya yi nauyin da ba za su iya kyalewa ba.

Sun ce Kungiyar Gwamnonin Arewa na bakin kokarin ta wajen hada hannu da gwamnatin tarayya domin ganin an dakile Boko Haram.

Sun ce tilas a binciki Mailafia a ji wanda ya ba shi labarin zargin gwamnan da ke daukar nauyin Boko Haram.

Share.

game da Author