Kodinatan shirin dabarun bada tazarar haihuwa ta jihar Bauchi Aisha Abdulkarim ta bayana cewa mata da dama a jihar sun fi su garzaya asibiti domin karbar kwayoyin bada tazarar haihuwa cikin dare.
Aisha ta fadi haka ne ranar Alhamis da take hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a karamar hukumar Toro.
” Da zarar 7 zuwa 8 na dare yayi zaka ga mata na garzayowa asibiti domin karbar wata dabara dake musu aiki na bada tazarar iyali. Sukan faki idon mazajen su ne.
Matan auren dake karamar hukumar Toro sun shaida cewa su kan yi haka ne domin a lokacin mazajensu na wauri daya, ba za su gan su ba a lokacin da suka fita neman magani. Sannan kuma tace wasu mazan ma da kan su suke rako matan su karbar maganin a asibiti.
Idan ba a manta ba cibiyar ‘Development Research and Project Centre (dRPC)’ ta shirya taro domin tattauna hanyoyin bunkasa amfani da dabarun bada tazarar iyali a Najeriya.
Jami’in dRPC Emmanuel Abanida ya bayyana cewa har yanzu dai mutane musamman mata na gudun amfani da dabarun bada tazarar iyali a Najeriya.
Hakan na da nasaba be da rashin amincewar wasu mazan domin Mata su kaiyade iyali.
Abanida ya ce bincike ya nuna cewa kashi 11 bisa 100 na mata a Najeriya ne kacal ke amfani da dabarun.
Ya ce kamata ya yi mutane su gane cewa amfani da dabarar bada tazaran iyali hanya ce dake taimakawa wajen inganta kiwon lafiyar mace da na yara.
” Ya zama dole fannin kiwon lafiya tare da masu fada a ji a fanin su zage damtse wajen ganin an wayar da kan mutane game da mahimmancin amfani da dabarun bada tazaran iyali.
Amfani 4 da dabarun tazaran iyali ke da shi
1. Yana inganta kiwon lafiya mace ganin cewa dabaran tazaran iyali hutu ne da mata ke samu kafin su sake haihuwa.
2. Inganta kiwon lafiyar yara saboda mace za ta sami lokacin kula da danta yadda ya kamata kafin ta sake w2ani haihuwan.
3. Hana yawan mace macen mata da yara kanana.
4. Amfani da dabaran tazaran iyali na han
Discussion about this post