Afrika za ta karbi shaidar yin sallama da cutar Shan-Inna a watan Agusta – WHO

0

Ofishin Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya WHO dake Brazzaville, kasar Kongo ta bayyana cewa Afrika za ta Samu shaidar rabuwa da cutar Shan Inna a Agusta.

Afrika za ta samu wannan shaida ne bayan gamsuwar da Kungiyar yaki da cutar shan inna (POLIO) ta Nahiyar Afrika (ARCC) ta yi game da ingancin yaki da cutar da ake yi a yankin.

Kasashen Afrika da za su samu wannan shaida na yin sallama da cutar Shan-Inna sun hada da Sudan ta Kudu, Afrika ta Tsakiyar, Kamaru da Najeriya.

Samun shaidar rabuwa da cutar a Afrika zai sa nahiyar Afrika ta shida da kenan cikin nahiyoyin duniya da suka samu itin wannan shada.

Najeriya na gab da samun shaidar yin sallama da cutar Shan-Inna – WHO

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa Najeriya na gab da samun shaidar rabuwa kwata-kwata da cutar shan-inna a Nahiyar Afrika.

WHO ta ce Najeriya ta kai ga Wannan matsayin ne a dalilin gamsuwar da Kungiyar yaki da cutar shan inna (POLIO) na kasashen Afrika (ARCC) ta yi game da ingancin kokarin kawar da cutar da gwamnatin kasar take yi.

Shugaban Hukumar cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko ta kasa (NPHCDA) Faisal Shu’aib a shafinsa na twitter ‘@drfaisalshuaib’ ya bayyana farin cikin sa kan wannan nasara da aka samu.

Najeriya ta yi nasara a haka ne a dalilin namijin kokarin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta yi da dinbbin tallafin da kasar ke samu daga gidauniyar Bill da Melinda Gates da gidauniyar Dangote.

Idan ba a manta ba a watan Disambar 2019 Kodinatan shirin yi wa yara allurar rigakafi a karkashin hukumar WHO Pascal Mkand ya ce Najeriya za ta iya samun shaidar rabuwa da shan inna kwata-kwata idan daga yanzu zuwa karshen shekaran 2020 ba a samu rahoton bullowar cutar a kasar ba.

Mkanda yace hakan zai tabbata ne idan kwamitin ERC ta gamsu da ingancin kokarin kawar da cutar da gwamnatin kasar take yi.

Share.

game da Author