SHEKARU 11: Kasuwancin hadin-guiwar NTA da Star Times bai tsinana ribar ko kwandala ba – Shugaban NTA

0

Majalisar Dattawa ta zaz-zare wa Shugabannin Gidan Talbijin na Najeriya (NTA) jajayen idanu, saboda shekara 11 da NTA ta bata ta na kasuwancin hadin-guiwa da kamfnin Start Times, ba tare da samun ribar ko kwandala ba.

Kamfanin Star Times mallakar wasu ‘yan Chana ne da ke hada-hadar harba tashoshin talbijin a manhajojin rariyar likau a duniya a Afrika da kuma satilayit a duniya, bisa tsarin zamani.

Shugaban Kwamitin Hadin Guiwar Kwamitin Harkokin Kudade da Tsare-tsare na Kasa, Solomon Adeola, shi ne ya bai wa Shugaban Gidan Talbijin na NTA takardar gargadi da neman sanin dalla-dallar yadda hulda tsakanin NTA da Star Times ta rika gudana har tsawon shekaru 11.

Shugaban NTA Yakubu Ibn Mohammed ya bayyana a gaban kwamitin ne a ranar Litinin a Abuja.

Sanata Adeola ya ce, “Shugaban NTA, ka na nufin ka na shaida mana cewa tsawon shekara 11 kasuwancin hadin-guiwa tsakanin NTA da Star Times, bai tsinana ko ribar naira daya tal ba?

“Ka na nufin duk banza kenan Star Times ke amfani da kayan NTA har mutum sama da milyan daya ke kallon tashoshi?

“In dai haka ne a gaskiya ba a yi wa ‘yan Najeriya adalci ba ko kadan. Ya zama tilas ka dawo mana tare da Shugaban Kula da Star Times kowa ne shi, domin mu yi abin da shi zai bayyana mana da bakin sa.”

Yayin da ya ke magana, Shugaban NTA ya ce, “Ina Babban Darakta a 2009. Amma a sani na, a lokacin ba a ci ribar ko kwandala ba a hadin-guiwar NTA da Star Times.

“Kuma daga zama na Shugaban NTA a 2016 zuwa yau ma babu riba ko ta sisin kwabo.

“Ni ma wannan tambaya ce na fara yi, a farkon hawa na shugabancin NTA cikin 2016.

“Har yanzu kuma haka ake ta mirginawa ba tare da samun riba ko ta sisin kwabo ba.”

Akan haka ne aka ce Shugaban NTA din ya koma gaban kwamiti a ranar Talata, tare da Manajan Daraktan Kasuwsncin NTA, Maxwell Loko, wanda shi ne ke kula da harkokin kasuwancin hadin-guiwar NTA da Star Times.

Share.

game da Author