‘Yan sanda sun damke Wata mata Fatima Bashir, mai shekaru 22 da shirya sace ‘yarta mai shekaru biyar don ta kala wa tsohon mijinta a kamashi.
An gano ta aikawa tsohon mijinta tes na ya biya kudin fansa na naira miliyan 2 kafin a saki ‘yar.
Kakakin ‘yan sandan jihar Katsina Gambo Isah, ya shaida wa manema labarai cewa ranar 5 ga watan Yuli, Fatima ta kawo karar an sace ‘yarta mai shekaru 5, kuma tana zargin tsohon mijinta ne ya sace yarinyar.
Gambo ya ce jami’ai sun gano cewa ashe Fatima ce ta rubutawa tsohon mijin ta tes tana neman ya biya naira miliyan 2 kudin fansa.
Sannan kuma da kanta ta shaida wa ‘yan sada a lokacin bincike cewa, ta gudu da ‘yar zuwa kano inda ta boyeta, tare da wata kawarta, Faiza.
Daga baya kuma sai ta maida ta Dutsi domin a ci gaba inda aka gano itace ta sace ‘yarta.
A karshe, Gambo ya ce ana nan ana ci gaba da bincike akai.