Shugaban jami’ar Maryam Abacha dake Maradi, kasar Nijar, ta karrama dalibarta da kyautar naira miliyan daya saboda kyawawan halayenta a lokacin da take karatu a makarantar.
Baya ga kyawawan halayenta, da dabiu masu kyau da ta ke da shi, tana da hazakar gaske a wajen Karatu.
Dalibar mai suna Maryam Damban ta kammala karatunta na gigiri a fannin Shari’a, a jami’ar MAAUN din.
Maryam ta cira tuta a karatunta inda ta zarce kowa ta fito da sakamakon ‘First Class’.
Da yake mika wa Maryam wannan kyauta ta naira milyan 1, Shugaban Jami’ar Farfesa Adamu Gwarzo, ya shaida cewa Jami’ar, ba karatu kawai bane jarumtar da jami’ar ke kula da, harda kyawawan dabi’u.
Ya yi kira ga sauran dalibai su yi lkoyi da kyawawan halin Maryan domin samun shaida irin haka.
Sannan kuma ya bata tallafi na musamman domin ci gaba da karatunta har digirin digir-gir, wato PhD.
Jami’ar MAAUN na gina jami’ar a Najeriya, sannan kuma tuni har ta fara karatu a Kwalejin koyan aikin Asibiti da Ungozoma dake Kaduna a Najeriya.