FYADE: Kotu ta daure mai gadi na tsawon shekara 9 a gidan Kaso

0

Kotun majistare dake Igarra jihar Edo ta daure Sunday Akpeji Mai shekaru 31 a kurkuku bayan ta kama shi da laifin yi wa ‘yar shekara 7 fyade.

Lauyan da ya shigar da karar Obeze Samuel ya ce Akpeji ya aikata wannnan laifi ne ranar 19 ga watan Agusta 2019 a gadin da yake yi a kwatas din Uffa dake Enwan/Ososo a karamar hukumar Akoko.

Ya ce Akpeji ya danne wannan yarinyar a dakinsa na mai gadi bayan ta fito waje daga gida don ta yi fitsari da dare.

Samuel ya gabatar a kotu shaidu da suka tabbatar cewa Akpeji ya aikata haka.

Bayan haka ne alkalin kotun Nosa Musoe ya yanke wa Akpeji hukuncin zama a kurkuku na tsawon shekara 9 ba tare da beli ba.

Musoe ya ce za a daure Akpeji a kurkukun Auchi.

Idan ba a manta ba a ranar 21 ga watan Yuli ne Babban kotu dake garin Ado Ekiti jihar Ekiti ta yanke wa mahaifin wasu ‘yan mata biyu da ya rika lalata da su mai suna Imole Akintewe dake da shekaru 65 a duniya hukuncin zama a kurkuku na tsawon shekara biyar bayan ta kama shi da laifin yi wa ‘ya’yansa Mata biyu fyade.

Alkalin kotun John Adeyeye ya ce ya yanke wa Akintewe wannan hukunci ne saboda tsawon shekaru da yake dashi da rokon sassauci da yi.

Alkalin Adeyeye ya ce Akintewe zai yi zaman gidan kaso ba tare da beli ba na tsawon shekaru 5.

A lokacin zaman kotun, lauyan da ya shigar da karar Felix Awoniyi, ya bayyana cewa Akintewe ya aikata wannan laifi ne ranar 28 ga Mayun 2019.

Share.

game da Author