NADA FANI-KAYODE: Masu rike da sarautun gargajiya Uku sun ajiye nadi a masarautar Shinkafi

0

Wasu masu rike da sarautun gargajiya a Shinkafi, jihar Zamfara sun ajiye mukamansu don bayyana fushin ga nadin tsohon ministan sufurin jiragen saman Najeriya, Femi Fani-Kayode “Sadaukin Shinkafi” da Sarkin Shinkafi Mohammed Makwashe yayi.

A wasika ajiye nadin sarautun su da suka yi kuma suka aika wa sarki Makwashe, sun shaida masa cewa basu tare da shi a nadin Fani-Kayode Sadaukin Shinkafi da yayi.

Wadanda suka ajiye nadin sun hada da, Bilyaminu Yusuf (Sardaunan Shinkafi); Umar Ajiya (Dan-Majen Shinkafi) da Hadiza Abdul’aziz-Yari (Iyar Shinkafi).

Sun koka cewa masarautar ba ta kyauta nada Fani-Kayode sarautar Sadauki ba a masarautar.

Sarki Makwashe, ya ce ya nada shi sarautar Sadauki ne ganin irin gudunmawar da ya ba masarautar da soyayya da ke tsakanin sa da masarautar.

Sai dai kuma sarakan da suka ajiye nadi, sun ce basu ga wani abin da yayi wa masarautar ba da za a yi masa sarautar sadauki. A dalilin haka suka ce ko dai a canja shawara a warware masa wannan nadi, ko kuma su gashi sun hakura da sarautar su.

Sannan kuma sun yi kira ga sauran masu sarauta a masarautar, su ajiye nadin su ma kamar yadda suka yi.

Share.

game da Author