KORONA: Abuja 86, Kaduna 56, Kano 17, yanzu mutum 38,344 suka kamu a Najeriya

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 543 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Laraba.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –180, FCT-86, Kaduna-56, Edo-47, Ondo-37, Kwara-35, Ogun-19, Rivers-19, Kano-17, Ebonyi-16, Enugu-16, Delta-7, Bayelsa-4 Bauchi-3 da Abia-1

Yanzu mutum 38,344 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 15,815 sun warke, 813 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 21,716 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 13,806 FCT – 3,297, Oyo – 2,219, Edo – 2,064, Delta – 1,444, Rivers – 1,565, Kano –1,447, Ogun – 1,203, Kaduna – 1,267, Katsina –713, Ondo – 1001 , Borno –603, Gombe – 558, Bauchi – 534, Ebonyi – 715, Filato – 762, Enugu – 721, Abia – 527, Imo – 454, Jigawa – 322, Kwara – 706, Bayelsa – 326, Nasarawa – 289, Osun – 359, Sokoto – 153, Niger – 166, Akwa Ibom – 176, Benue – 294, Adamawa – 115, Anambra – 132, Kebbi – 90, Zamfara – 77, Yobe – 64, Ekiti – 86, Taraba- 54, Kogi – 5, da Cross Rivers – 29.

Babu abinda ya hada Korona da zazzabin cizon sauro – Hukumar NCDC

Hukumar Hana Yaduwar Cututtuka Ta Kasa NCDC ta bayyana cewa babu abinda ya hada cutar Korona da zazzabin cizon sauro.

Hukumar ta ce kwayoyin cututtukan dake haddasa cutar covid-19 ba shine ke kawo zazzabin cizon sauro ba.

Masana kimiyya sun bayyana cewa kwayoyin cutar SARS-CoV ne ke kawo cutar covid-19, sauro kuma ke kawo zazzabin maleriya.

Alamun cutar covid-19 sun hada da rashin iya numfashi yadda ya kamata, zazzabi, ciwon makogoro, tari ko atishawa, yawan jin kasala a jiki, rashin iya jin dandano abinci da kamshi, gudawa, mura da sauran su.

Shi kuma alamun zazzabin cizon sauro sun hada da ciwon Kai, yawan yin zufa, ciwon gabobbin jiki, amai, suma, yawan Jin kasala da kuma masassara.

Share.

game da Author