Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta gargadi mutane da su daina amfani da takunkumin rufe baki da hanci a lokacin da suke motsa jiki.
WHO ta ce saka takunkumin fuska na hana mutum shakar iska da kyau ba.
Kungiyar ta ce takunkumin fuska na iya jikewa da zufa idan aka yi amfani da shi a lokacin da ake motsa jiki, kuma hakan hadari ne ga lafiyar mutum.
Abin da ya kamata mutum ya Yi shine idan ya fito waje domin motsa jiki ya tabbatar ya ba da rata tsakaninsa da sauran mutane a kalla mita daya.
Bayan haka WHO ta karyata camfin da wasu mutane ke yi cewa takunkumin fuska na hana a shaki iskar da ya kamata wato ‘ Oxygen’ maimakon haka iskar da bai kamata bane zai rika shaka wato ‘Carbon-dioxide’.
“Idan mutum na amfani da takunkumin rufe baki da hanci ya tabbatar ya toshe duk wata kafa da iska za ta shiga ba tare da ya takura ba wajen shakar iska.
“Ba a maimaita takunkumin rufe baki da hanci da likitoci ke amfani da shi kokuma Wanda ake kira disposable mask, yarwa ake yi bayan an kammala amfani da shi.
“Sannan idan disposable mask ya jike a yar kada a ci gaba da amfani da shi a saka sabo.
Kungiyar ta ce kwayoyin cutar coronavirus ba su zama a takalma musammam wadanda aka fita da su.
” Domin kare kiwon lafiyar yara kanana musamman na goye a kebe wuri na musamman domin ajiye takalman da aka fita da su.
WHO ta ce maganin inganta karfin garkuwan jiki wato ‘ Antibiotics’ ba ya maganin cutar coronavirus.
Mai fama da cutar coronavirus zai iya kamuwa da kwayoyin cututtukan ‘Bacteria’ Wanda antibiotics zai iyakwar da shi.
Kungiyar ta yi kira ga mutane da idan sun ji canji a jikin su su hanzarta zuwa asibiti domin yin gwajin cutar Coronavirus.