FALLASA: Minista Keyamo dan jagaliya ne, shi ya sa ya yi bambami a Majalisa – Sanata Ubah

0

Sanata Ifeanyi Ubah daga Jihar Anambra, ya bayyana bobbotan da Karamin Ministan Kwadago, Festus Keyamo ya yi a Majalisar Dattawa da cewa dabi’a ce ta dan jagaliya da ‘yan tasha.

Ya ce ya na mamakin yadda Keyamo ya rika hauragiyar tunanin cewa Sanatoci na kokarin kwace daukar ma’aikata aiki daga hannun sa.

Ya yi wannan raddi ne a wata tattaunawa da manema labarai a Abuja, ranar Laraba, inda ya yi matashiya cewa aikin Sanatoci shi ne sa-ido kan ayyukan da Ministoci ke yi, kuma shi Keyamo din ya san haka.

PREMIUM TIMES ta buga lanarin yadda Keyamo ya rika hayagaga da bambami a zaman sa Kwamitin Ayyuka na Majalisar Dattawa a ranar Talata.

An shirya taron ne domin su san inda aka kwana game da batun daukar ma’aikata 774,000 da gwamnatin tarayya ta ce za ta dauka aiki.

A cikin Kasafin 2020, Majalisar Dattawa ta amince da kashe naira bilyan 52 wajen biyan wadannan ma’aikata da kuma ayyukan da za su rika yi a fadin kasar nan.

Za a dauki ma’aikata 1,000 a kowace Karamar Hukuma a fadin kasar nan cikin Kananan Hukumomi 774.

Keyamo ya zargi Sanatoci da kokarin yin babakeren kwace yawan da za a dauka, duk kuwa da cewa an ba su alfarmar kawo wadanda za a dauka aikin har adadin kashi 15% daga cikin 774, 000 da za a dauka aikin.

Sanata Ubah ya ce Sanatoci ba su yi laifi ba don sun tambayi yadda aka raba daukar ma’aikatan.

A matsayi na na sanatan da ke wakiltar jama’a, hakki na ne na binciki yadda ya ke tafiyar da tsarin daukar ma’aikata a kasar nan. Saboda abin ya shafi wadanda na ke wakilta. Sannan kuma wanda aka damka wa aikin daukar ma’aikatan ba cikakken Minista ba ne, na je-ka-na-yi-ka ne.

“Ni ban san abin da Minista ke nufi ba, da ya yi kane-kane wajen daukar ma’aikatan da za a rika biya ladar naira 20,000 ko 30,000 a wata ba. In banda dan tasha da dan jagaliya, ya daga mun yi maka tambaya za ka kama cika ka na batsewa, ka na ihu da kwaratsatsa?

“Mu ne ya kamata a bai wa damar dauka ko kawo sunayen wadanda za a dauka.

“Amma damka aikin a hannun dan jagaliya da zai je ya yi harkallar raba guraben ayyukan, abu ne da ba za mu amince ba.”

Share.

game da Author