Ofishin EFCC na Shiyyar Abuja, ya bayyana cewa ya kwato zunzurutun kudade har naira bilyan 1,541,801,872 a Abuja tsakanin watan Juni 2019 zuwa Yuni 2020.
Da ya ke jawabi a ranar Laraba wajen taron manema labarai, inda ya bayyana ci gaban shiyyar, Shugaban Shiyyar Abuja, Aminu Aliyu, ya ce makudan kudaden ba su ke nan ba.
“Akwai dala 10,386 sai fam na Ingila 730,500.”
EFCC ta yi bayanin wannan kamen kudaden da ta yi a Abuja bayan ofishin ta na Sokoto ya sanar da kwato naira milyan 400 daga wasu barayin gwamnati.
Aliyu ya ce an daga cikin kudaden da aka kwato a Abuja, an samu naira milyan 315,825,431 daga daidaikun mutane daban-daban. Yayin da aka kwato wasu naira milyan 285, 430, 343 daga hadakar kamfanoni ko gungun jama’a.
Ya ce an kwato wa Gwamnatin Tarayya naira milyan 940, 546, 098.
Aliyu ya ce da taimakon jami’an binciken-kwakwaf na Amurka, wato FBI, an samu damke wasu rikakkun ‘yan harkalla su uku.
“An kuma kwato kadarori da motoci a cikin wadannan kudaden, wadanda duk an damka su a hannun gwamnatin tarayya.”
Aliyu ta ce a cikin shekara daya din, sun karbi takardun korafe-korafen inda aka sack kudade har 704, sun kama mutum 314.
Bayan sun tantance korafe-korafen, sun yi watsi da wadanda ba sahihai ba. An gurfanar da mutum 67 a kotu, kuma har an yanke wa mutum 43 hukunci.
Ya ce EFCC ta yi wannan kokari ne duk kuwa da cewa ma barkewar cutar Coronavirus ya kawo wa aikin na ta cikas da jinkiri.
A karshe ya kara rokon ‘yan jarida da ‘yan kunguyoyin kare dimokradiyya su ci gaba da bai wa EFCC hadin-kai wajen yaki da cin hanci da rashawa a kasar nan.