Sakamakon binciken da PREMIUM TIMES ta gudanar ya nuna cewa adadin yawan mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a babban birin tarayya, Abuja da jihar Legas ya fi yawan mutanen da suka kamu da cutar a sauran jihohi 34 dake kasar nan.
Bisa ga sakamakon gwajin da Hukumar NCDC ta gabatar ya nuna cewa adadin yawan mutanen da suka kamu da cutar a Abuja da Legas sun kai 8,785 ko kuma kashi 51 bisa 100 sannan adadin yawan mutanen da suka kamu a jihohi 34 dake kasar nan sun kai 8,363 ko kuma kashi 48.7.
Jihar Cross Rivers ne jihar da har yanzu ba a samu rahotan bullar cutar ba.
A lissafe dai mutum 7,461 ne ke dauke da cutar a jihar Legas sannan mutum 1,324 a Abuja.
Daga nan sai jihar Kano wanda ke da mutum 1,158, mutum 631 a Ribas, Edo mutum 620, Ogun 574, Kaduna 472 da Borno 445.
Mutum 3 na dauke da cutar a jihar Kogi, Taraba mutum 18, sannan 30 a jihar Ekiti.
Gwamnati jihar Kogi ta musanta mutum ukun da aka ce wa sun kamu a jihar.
Mutum 17,148 ne ke dauke da cutar a Najeriya bisa ga sakamakon gwajin da Hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba da yamma.
An sallami mutum 5,623 sannan mutum 455 sun mutu a kasar nan ranar Talata.
Gwajin cutar
Duk da yawan mutane da suka kamu da cutar ma’aikatan kiwon lafiya sun yi kira ga gwamnati da ta kara yawan gwajin da ake yi wa mutanen kasar.
Tun da cutar ta bullo a watan Fabrairu mutum 96,402 ne aka yi wa gwajin cutar a kasar nan.
A ranar Laraba hukumar NCDC ta ce ta kara bude wuraren yin gwajin cutar guda hudu a kasar nan.
Hukumar ta kuma ce gwamnati za ta bude sabbin wuraren yin geaji biyu a jihohin Gombe da Ondo.
Zuwa yanzu akwai wuraren yin gwajin cutar 38 a kasar nan.
Sai dai duk da yawan wuraren gwajin da ake da su a kasar Hukumar NCDC bata cimma burinta ba na iya yi wa mutum miliyan biyu gwajin cutar cikin watanni uku.
Har yanzu hukumar bata yi wa mutum 100,000 gwajin cutar a kasar nan.
Kasashen Afrika
A kasar Afrika ta Kudu dake da yawal al’umma mutum miliyan 59, ta yi wa mutum sama da miliyan daya gwajin cutar.
Daga ciki mutum 76,334 suka kamu da cutar.
A kasar Morocco dake da yawan al’umma miliyan 36, ta yi wa mutum 400,000 gwajin cutar inda mutum 8,997 suka kamu da cutar.
A kasar Masar da ke da alumma sama da miliyan 100, ta yi wa mutum 135,000 gwajin cutar, ciki mutum 47,856 suka kamu.
A kasar Ghana dake da yawan al’umma miliyan 31 ta yi wa mutum 250,000 gwajin cutar mutum 12,590 daga ciki suka kamu.
A Najeriya gwamnati na ci gaba da sassauta dokar garkame mutane da aka yi amma kuma, abin ya zama kamar ci gaban mai hakan rijiya, domin ana sassautawa ne ana kuma samun karin yawan wadanda suka kamu da cutar da yafi a lokacin da aka saka dokokin.