ZABEN EDO: INEC ba za ta kara wa’adin zaben-fidda-gwani da ranar maida fam din takara ba -Yakubu

0

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa INEC ba za ta kara wa’adin kwanakin gudanar da zaben-fidda-gwanin ‘yan takara na zaben gwamnan jihar Edo ba.

Da ya ke bayani a Abuja, Yakubu ya ce haka kuma ba za a kara wa’adin ranar da kowane dan takara zai maida fam din sa ba.

Wannan bayani ya zo ne daidai lokacin da jam’iyyar APC ta afka cikin kakudubar rigimar da ta kai an ki tantance Gwamna Obaseki, shi kuma ya fice daga jam’iyyar, shi da mataimakin sa.

Kwana daya bayan ficewar ta sa, Babbar Kotun Daukaka Kara ta sauke Adams Oshiomhole daga shugabancin APC na kasa, inda jam’iyyar ta nada tsohon gwamnan Oyo, Abiola Ajimobi shugabancin riko.

INEC ta ce akwai jam’iyyu 15 da suka yanki fam na takarar zaben gwamnan Edo, wanda za a gudanar a ranar 19 Ga Satumba, 2020.

“Kowane dan takara zai tabbatar da ya cewa ya maida fam fam din sa a ofishin mu nan da 29 Ga Yuni, kafin karfe 6 na yamma.

“Batun zaben-fidda-gwani kuwa, kowace jam’iyyar da ta shiga takara ta tabbatar ta kammala zaben ta nan da kwanaki 10, wato zuwa ranar 27 Ga Yuni, 2020.

“Gudanar da zaben-fidda-gwani aikin jam’iyya ne. Amma dai INEC za ta tura jami’an ta domin sa-idon ganin yadda zaben zai gudana.” Inji Yakubu.

Ya kuma ka hankalin jam’iyyu cewa su tabbatar sun tsaida ‘yan takarar da suka cika sharuddan INEC hudu, don gudun kada a rika fadi-tashin tafiya kotu zaman kararraki bayan zabe.

Share.

game da Author