Shafin yanar gizon Ofishin Shugaban Kasa cike ya ke fal da tarkacen tsoffin bayanan da ba su dace a gani ba

0

Shafin yanar gizo na Ofishin Shugaba Muhammadu Buhari cike ya ke fal da tarkacen tsoffin bayanai, wadanda tuni lokacin su ya shude.

Shafin mai suna statehouse.gov.ng a cukurkude ya ke tsoffin sunayen wasu da tuni ba suka bar aiki a Fadar.

PREMIUM TIMES ta leko cewa har yanzu sunan marigayi Abba Kyari ne sunan sa matsayin Shugaban Ma’aikatan Ofishin Shugaban Kasa, maimakon sabon wato Farfesa Ibrahim Gambari.

Abba Kyari da Buhari ya nada ranar 27 Ga Agusta, 2015, ya rasu sanadiyyar cutar Coronavirus a ranar 1 Ga Agusta.

Buhari ya sake nada sabo, Farfesa Gambari cikin watan Mayu. Amma kuma a shafin yanar gizon ofishin Buhari, har yau Kyari ne a rubuce.

Haka duk da an yi wa Babban Sakataren Fadar Shugaban Kasa Jalal Arabi canjin wurin aiki, har yau sunan sa ne matsayin Babban Sakataren Fadar Shugaban Kasa.

Tun cikin watan Maris Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Folashade Esan ta cire Arabi ta maida shi Babban Sakataren Ma’aikatar Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwar Marasa Galihu.

An maye gurbin Arabi da sunan Tijjani Umar, Amma har yarzu babu sunan Umar a shafin intanet na yanar gizon Fadar Shugaban Kasa, wato State House.

An canja Festus Keyamo daga Karamin Ministan Hukumar Bunkasa Yankin Neja Delta. Amma har yanzu a shafin yanar gizon, sunan Keyamo ne a kai.

An dai maida Keyamo Karamin Ministan Kwadago da Inganta Ma’aikata.

An canja Keyamo ya koma inda aka cire Karamin Ministan Kwadago Festus Alasoadura. Yanzu Alasoadura ne Karamin Ministan Hukumar Bunkasa Yankin Neja Delta.

Amma a shafin intanet na Fadar Shugaban Kasa har yau ba a shigar da wannan canji ba, wanda aka yi tun a ranar 24 Ga Satumba, 2019.

Share.

game da Author