Uwargidan shugaban Kasa Aisha Buhari ta koka da kakkausar murya yadda aka yi awon gaba da ADCn ta da jami’ai masu kare ta aka garkame su ba tare da an sanar da ita ba.
Aisha ta ce ” Yanzu dai na kira sufeto janar din ‘Yan sanda domin a saki masu kare da aka garkame a kurkuku domin kare su daga hadarin kamuwa da cutar COVID-19.
Cikin wadanda aka tsare, akwai ADCn Aisha, Usman Shugaba da da wasu masu kare uwargidan shugaban kasan.
Bayanai sun nuna cewa akwai yiwuwar an tsare wadannan masu kare uwargida Aisha ne bayan cacan baki da ita kanta ta yi da wani daga cikin hadiman shugaba Buhari saboda tilasta wa wani hadiminta ta ya killace kansa bayan ya dawo daga tafiya.
Shidai ADCn Aisha yayi tafiya ne sannan bayan ya dawo sai aka shawarce shi da ya killace kan sa na kwanaki kafin ya shigo fadar shugaban kasa. ADCn ya banzatar da wannan gargadi ya ci gaba da zuwa aiki.
Daga nan sai maganan ya koma kunnen Aisha, ita kuma ta tunkari wannan hadimin shugaban kasa inda suka kaure da cacancan baki, wasu daga cikin masu kare ta suka saka baki nan take suma.
Kakakin Aisha Buhari, Aliyu Abdullahi, ya tabbatar da aukuwar wannan al’amari inda ya ce ba a kyauta wa uwargidan shugaban kasa ba tsare masu kare ta kai tsaya ba tare da ta sani ba.
” Ya dai kamata a ce kafin a tsare wani mai kare matar shugaban kasa, annsanar da ita tukunna, ba kawai a yi awon gaba da ita ba, ita kuma ko oho.
Abdullahi ya ce ba a yi abinda ya dace kuma ba a daraja ofishin ta da matsayinta na maidakin uwargidan shugaban kasa ba.
Discussion about this post