Majalisar Dattawa za ta bada sammacin damko mata Minista Lai Mohammed da wasu ministoci

0

Kwamitin Majalisar Dattawa Mai Binciken Yadda Ake Kashe Kudaden Hukumomin Gwamnatin Tarayya (Public Account Committee), ya yi barazanar umartar jami’an tsaro su damko Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed da wasu ministoci da shugabannin bangarorin hukumomi da ma’aikatun gwamnatin tarayya.

Hakan ya biyo bayan bijirewar da suka yi na kin amsa kiran Kwamitin Bincike da wasikar Akanta Janar na Tarayya

An gayyace su ne domin su bada bayanin lungunan da wasu bilyoyin kudade suka makale a ma’aikatun su, tun a wani bincike na kudaden da suka kashe a 2015, amma suka ki halarta.

Sauran sun hada da Ministan Harkokin Man Fetur, Ministan Albarkatun Karkashin Kasa, Ministan Harkokin Lantarki da kuma Ministar Harkokin Mata.

Akwai kuma Shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa a cikin jerin sunayen wadanda ake neman su bayyana, amma sun noke.

“Sama da wata daya kenan mu na bin su day lalama, an rubuta masu wasiku domin su zo su yi bayanin inda kudaden suka makale, tun 2015, amma sun ki bayyana.

“Wannan rashin da’a ce kuma rashin mutunta aikin su da raina dokar kasa.

“Saboda sun raina ‘yan Najeriya da gwamnatin kan ta, babu wani kwakkwaran dalilin da suka aiko na kin bayyana su yi bayani.

“Akwai wadanda suka raina wa mutane wayo, suka bayar da dalili na wofi da rashin mutunci.

“Lai Mohammed ya rasa dalilin sa na kin bayyana a gaban mu, sai ya aiko wai ‘yan kwangilar da aka bai wa aiki na kudaden da ake nema ne ba su nan.”

Haka Shugaban Kwamitin Bincike, Sanata Mathew Urhoghibe, dan PDP daga Jihar Edo ya bayyana.

Sauran kuma saboda rashin ta-ido, sai suka ce wai a karon farko kenan suka fara ganin takardar gayyata domin yin karin bayanin.”

Ya ce Dokar Sashe na 89 ya bai wa Kwamitin Bincike na Majalisar Dattawa ikon sa “a kamo mata ko minista ko ma wani gagararre ko bijirarren shugaban wata ma’aikata domin zuwa ya yi bayanin salwantar wasu kudade.”

Sanatan ya kara da cewa kudaden da ake binciken yadda aka kashe su, ba kadan ba ne, makudan bilyoyi ne.

Sauran ‘yan kwamitin da shi ma Akanta Janar duk sun goyi bayan a kamo wadanda suka ce guduwa suka yi suka ki bayyana.

Share.

game da Author