Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 403 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Juma’a.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Juma’a sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum – 68, Gombe-73, Kano-46, Edo-36, FCT-35
Nasarawa-31, Kaduna-17, Oyo-16, Abia-15, Delta-13, Borno-13, Plateau-8, Niger-7, Ribas-7, Enugu-6, Ogun-6, Kebbi-3, Ondo-1, Anambra-1
Imo-1
Yanzu mutum 16,085 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 5,220 sun warke, 420 sun rasu.
Duk da yawan mutane da ake samu sun kamu da cutar a kullum a Najeriya, wasu da dama na ganin har yanzu ba a yi wa mutane gwajin cutar yadda ya kamata a kasar.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 7,103, sai FCT – 1, 247, Kano – 1, 137, Ogun – 559, Edo – 580, Oyo – 507, Rivers – 489, Kaduna – 446, Borno – 438, Katsina – 414, Bauchi – 410, Gombe – 410, Jigawa – 317, Delta – 267, Ebonyi – 162, Abia – 166, Kwara – 150, Plateau – 156, Nasarawa – 172, Imo – 136, Sokoto – 132, Zamfara – 76, Anambra – 65, Ondo – 64, Yobe – 55,Kebbi – 57, Enugu – 57, Osun – 50, Niger – 56, Akwa Ibom – 48 Adamawa – 42,, Benue – 34, Bayelsa – 32, Ekiti – 30, Taraba – 18, da Kogi – 3.
Discussion about this post