Anambra ta hada magungunan gargajiya har shida dake warkar da Korona

0

Mai ba gwamnan jihar Anambra shawara kan magungunan gargajiya Onyekachukwu Ibezim ya bayyana cewa gwamnati ta amince da wasu magungunan gargajiya har 6 dake da ingancin warkar da cutar Korona.

Ibezim ya fadi haka ne ranar Talata a garin Awka da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya.

Ya ce a yanzu haka gwamnati ta aika da Wadannan magunguna Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) dake jihar domin tantance su.

Ibezim ya ce sai da kwararrun likitoci a jihar suka tantance ingancin maganin kafin gwamnati ta amince da su sannan ta aika da Hukumar NAFDAC.

” Wadannan magungunan da suka hada da gari, kwayoyi da jikon itatuwa na da ingancin warkar da cutar Korona.

“Gwamnati ta kafa kwamiti domin tantance magungunan gargajiya a jihar wadanda a ke saida su a jihar.

Gwamnati ta yi kira ga masu siyar da magungunan gargajiya ba tare da izinin gwamnati ba da su gujin yin haka a jihar.

Mutum 73 ne suka kamu da cutar a jihar.

Mutum 25,133 ne ke dauke da cutar a Najeriya, mutum 9402 sun warke, 537 sun mutu.

Share.

game da Author